Kwamitin majalisar wakilai ya yaba da sake fasalin kiwon lafiya a jihar Jigawa

Kwamitin majalisar wakilai ya yaba da sake fasalin kiwon lafiya a Jigawa

Lafiya

Daga Aisha Ahmed 

Dutse, Aug. 22, 2025 (NAN) Kwamitin majalisar wakilai mai kula da harkokin kiwon lafiya, ya yabawa gwamnatin jihar Jigawa bisa bullo da sabbin tsare-tsare masu inganci a fannin kiwon lafiya. 

Shugaban kwamitin, Mista Amos Gwamna-Magaji, ya bayyana haka a lokacin da ya kai ziyarar ban girma ga Gwamna Umar Namadi,;a Dutse.

Ya yaba da irin nasarorin da aka samu a shirin kawo sauyi a fannin kiwon lafiya, musamman kashi 15 na kasafin kudin da aka ware wa fannin.

“Muna alfahari da farin cikin jin cewa sama da kashi 15 cikin 100 na kasafin kudi na shekara bana, don kiwon lafiya ne, wanda abin mamaki ne kuma ya yi tasiri.

“Duk da haka, mun kuma ga cewa sama da kashi 15 cikin 100 na kasafin, ba a takarda kawai yake ba, kashi 15 cikin 100 na kasafin kudin na yawo tare da sauya yanayin kiwon lafiya yadda ya kamata a jihar Jigawa,” inji shi.

Gwamna-Magaji ya taya gwamnan murnar samun kyautar kudi sama da dala 500,000 na PSC Leadership Challenge Award da jihar ta samu.

Yana mai bayyana hakan a matsayin hujjar daukakar kimarsa a garambawul na kiwon lafiya. 

“Wannan ya nuna jajircewar ku da kuma matsayin da kuka kai, da kuma abin da kuka yi a fannin lafiya,” in ji shi.

Shugaban ya kuma yabawa gwamnatin jihar, kan yadda aka daidaita albashin ma’aikatan lafiya da ma’auni na tarayya.

Ya kara da cewa, wannan wani gagarumin mataki ne na magance dakilewar kwakwalwar kwararrun likitoci.

Da yake mayar da martani, Namadi ya sake jaddada kudurin sauya fannin kiwon lafiya zuwa ga cimma nasarar da ake samu na kula da lafiya ta duniya (UHC) a jihar.

 A cewar Namadi, kiwon lafiya shine tushen ci gaban zamantakewa da bunkasar tattalin arziki da ci gaban al’umma. 

“Mun yi imanin cewa al’umma mai koshin lafiya al’umma ce mai ci gaba, tare da lafiya ne kawai za ku nemi ilimi, kuma ku bunkasa harkokin tattalin arziki don inganta tattalin arziki,” in ji shi.

Ya ce gwamnatinsa ta gudanar da bincike na kwakwaf, don jagorantar tsare-tsare da ba da fifiko a dukkan bangarori, tare da kula da lafiya a matsayin fifiko.

Namadi ya ce jihar ta mayar da hankali ne wajen karfafa ayyukan kiwon lafiya a matakin farko, da ke zama ginshikin samar da ingantaccen sabis. 

“Dole ne a karfafa kiwon lafiya na farko don samar da lafiya ga mutane. Mun tabbatar akwai bukatar samar da cibiyoyin kiwon daga tushe, inda ma’aikata da ‘yan ƙasa za su yi farin ciki,” in ji shi. 

Gwamnan ya bada tabbacin aniyar gwamnatin sa na zurfafa sauye-sauyen harkokin kiwon lafiya domin cimma nasarar UHC. (NAN) (www.nannews.ng)

 

 AAA// RSA 

Fassarar Aisha Ahmed

Hukumar Kwastam ta kama miyagun kwayoyi da kudinsu ya kai N690m a Katsina

 

Magunguna

Daga Abbas Bamalli

Katsina, Aug. 19, 2025 (NAN) Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, ta ce hukumar kwastam ta Najeriya ta kama miyagun kwayoyi da kudinsu ya kai kimanin Naira miliyan 690.

Rundunar ta ce sun tare wasu motoci guda biyu da ke dauke da kayayyakin.

Shugaban hukumar NCS a jihar, Mista Idriss Abba-Aji, ne ya bayyana hakan a Katsina ranar Talata, yayin da yake zantawa da manema labarai kan kama magungunan.

A cewarsa, jami’an ‘yan sanda sun kama katan 14 na Tramadol da kudinsu ya kai Naira miliyan 650 da kuma kafsul din Fragbaline na Naira miliyan 28, wadanda aka boye a cikin motoci daban-daban guda biyu.

Ya bayyana cewa an kama su ne a cikin makonni biyu, ya kara da cewa jami’an sun kwace tabar wiwi na kimanin naira miliyan 15.

“A ‘yan kwanakin nan, mun lura cewa ana amfani da iyakokinmu wajen safarar miyagun kwayoyi, ana amfani da motoci da wayo don rikitar da jami’an tsaro da ke cin karo da su.

“Kuna iya lura irin wadannan motoci na jigilar manyan mutane ne, jama’a su fahimci cewa a yayin gudanar da ayyukanmu, muna dakatar da duk wata mota don tabbatar da an duba lamarin.

“Mutane na korafin yadda kwastam ke damun masu ababen hawa, masu safarar muggan kwayoyi ba za su taba amfani da manyan motoci ko bude motoci ba.

“Suna boye muggan kwayoyi a cikin motocin da aka kera,” in ji Kwanturolan.

Ya jaddada cewa jami’an ba za su iya gano irin wannan boye-boye ba tare da tsayawa da bincike ba. A cewar sa, sun yi sa’ar kwace motoci biyu a lokuta daban-daban.

Abba-Aji ya lura cewa kowace mota na dauke da muggan kwayoyi masu yawa, wadanda ake zargin ana raba su a cikin Katsina da jihohin da ke makwabtaka da su idan ba a kama su ba.

“Kwanan nan, a daya daga cikin iyakokinmu, mun kama miyagun kwayoyi, musamman Tramadol, a cikin kwali 14 da kudinsu ya kai kimanin Naira miliyan 650.

“Wannan ne laifi mafi girma irinsa ga wannan rundunar,” in ji Abba-Aji.

 Ya ci gaba da cewa shaye-shayen miyagun kwayoyi na rura wutar rikicin ‘yan fashi a yankin.

Don taimakawa wajen dakile wannan barazana, rundunar ta kara kaimi wajen aiwatar da ayyukan ta.

A cewarsa, an kama mutum daya da ake zargi tare da daya daga cikin motocin, amma daga baya aka sake shi akan beli. (NAN) (www.nannews.ng)

AABS/KTO

 

Fassarar Aisha Ahmed

An gudanar da zaben cike gurbi cikin lumana a jihar Jigawa

Zabe

Daga Muhammad Nasir Bashir

Babura (Jigawa), Aug. 16, 2025 (NAN) An gudanar da zabe cikin lumana a zaben cike gurbi na mazabar Babura-Garki a Jigawa a ranar Asabar.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa tun da karfe 8:00 na safe, masu kada kuri’a suka yi dafifi zuwa rumfunan zabe, a daidai lokacin da jami’an tsaro ke da isasshen tsaro a fadin yankin.

Jami’an ‘yan sandan Najeriya (NPF), jami’an tsaro ta Civil Defence (NSCDC), Hukumar Shige da Fice ta Kasa (NIS) da sauran su, sun tabbatar da kiyaye doka da oda a rumfunan zabe da sauran muhimman wurare a Babura da Garki.

A rumfar zabe ta Garki Kofar Fada (003) da firamaren Yamma (005) a garin Garki, an ga jami’an zabe suna shirya kayan zaben tun kafin a fara da karfe 8:30 na safe.

Mista Ibrahim Shehu, jami’in zabe na 1 a rumfar zabe, ya ce sun yi isassun shirye-shirye domin saukaka gudanar da aikin.

Wani sashe na masu kada kuri’a sun yaba da yadda zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali, inda suka jin dadi ga yadda jami’an tsaro suka gudanar da aikinsu.

Zaben ya samu fitowar jama’a da dama da suka hada da ministan tsaro, Badaru Abubakar, da karamar Ministan Ilimi Hajiya Suwaiba Ahmad.

An kuma ga wasu mazauna yankin suna gudanar da harkokinsu na yau da kullum, yayin kada kuri’a cikin lumana a mafi yawan wuraren da aka ziyarta. (NAN) (www.nannews.ng)

 

MNB/ISHO/ RSA

Fassara Aisha Ahmed

Zaben cike gurbi: An kama mutane 100 bisa zargin bangar siyasa a Kano

Banga

Daga Aminu Garko

Bagwai (Kano) Aug.16, 2025 (NAN) Hukumar zabe mai zaman kanta a jihar Kano, ta tabbatar da cewa an kama sama da mutane 100 da ake zargin ‘yan bangar siyasa ne a karamar hukumar Bagwai yayin zaben cike gurbi da ake gudanarwa a jihar.

Kwamishinan zabe na jihar Kano, Mista Abdu Zango, ya tabbatar da faruwar lamarin, yayin da yake zantawa da manema labarai, bayan ya duba zaben da aka gudanar a garin Bagwai a ranar Asabar.

Ya ce an samu wadanda ake zargin dauke da makamai daban-daban, kuma Zango ya nuna jin dadinsa da yadda zaben ya gudana.

A cewarsa, an samar wa jami’an zabe kayayyakin da suka dace a duk wuraren da aka kebe.

Sai dai ya tabbatar da cewa an samu wasu tsaikon a harkar saboda al’amuran da suka shafi dabarun samun ingantaccen tsaro.

Ya ce akwai jami’an tsaro a dukkan wuraren zabe domin tabbatar da doka da oda tare da gudanar da zabe cikin lumana. (NAN) (www.nannews.ng)

AAG/ISHsa Ishola/Sam Oditah ne ya gya

 

Aisha Ahmed ta fassara

Mamakon ruwan sama yana yi mana barazana – manoman shinkafa a Abakaliki

 Douglas Okoro

Abakaliki, 6 ga Agusta, 2025 (NAN) Manoman shinkafa a Abakaliki, sun koka kan yadda ake samun mamakon ruwan sama, wanda a cewarsu yana barazana ga noman shinkafa a shekarar 2025.

Manoman, sun bayyana damuwar tasu ne a wata tattaunawa da suka yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a ranar Laraba a garin Abakaliki.

An dai samu mamakon ruwan sama a bana wanda ya yi sanadin ambaliya da asarar amfanin gona a manyan yankunan da ake noman shinkafa a jihar.

Mista Emmanuel Nwali, wani fitaccen manomin shinkafa a karamar hukumar Izzi, ya ce kusan rabin gonar shinkafarsa ta nutse sakamakon ruwan sama mai yawa.

“Ambaliya ta lalata yawancin gonakinmu, abin da ya rage tuni ya koma tawaya.

“Kusan kullum ana ruwan sama tun tsakiyar watan Yuli. Wataƙila ba za mu yi tsammanin samun girbi mai yawa a wannan kakar ba,” in ji Nwali.

Wani manomi, Mista Chinedu Okenwa, ya ce ya yi asarar gidajen yara na reno sakamakon ambaliyar ruwa, wanda ya yi sanadin asarar manyan albarkatu.

“Ban san yadda zan gyara asarar da aka yi ba, domin a halin yanzu, ba zan iya dasa komai ba don ya lalace.

“Muna fuskantar karancin amfanin gona a wannan kakar, kuma hakan na iya haifar da hauhawar farashin shinkafar gida a shekara mai zuwa,” in ji shi.

Hakazalika, Mista Aloysius Njoku, wani Mai nomana kasuwanci, ya ce ya yi asarar wani kaso mai yawa na gonar shinkafa sakamakon ambaliya, kuma yana fargabar ci gaban zai yi illa ga girbi.

“Damina da ambaliyar ruwa sun yi mummunar barna, idan ba a yi wani abu ba, shinkafa za ta yi karanci da tsada, kuma kowa zai ji ajikinsa,” in ji Njoku.

Misis Sylvia Elom, wata ma’aikaciyar gwamnati kuma mai noman shinkafa, ta bayyana ddamuwarta inda tace barnar da ruwan sama ya yi a gonaki ta yi kamari kuma abun zai shafi mutane da dama da suka dogara da noman shinkafa domin tafiyar da rayuwarsu.

“Shinkafa ita ce babbar hanyar samun kudin shiga ga yawancin mutanenmu wadanda galibi manoma ne, idan ambaliyar ruwa ta lalata mana gonakinmu, ba a bar mu da komai ba kenan,” in ji ta.

A halin da ake ciki, Dr Paul Onwe, wani kwararren manoma mai zaman kansa, ya bayyana cewa akwai gagarumar matsala a noman shinkafa idan damuna ta tsawaita aka samu ambaliya.

Ya kara da cewa ruwan sama kamar da bakin kwarya, yana haifar da babbar barazana ga gonakin shinkafa, musamman wadanda ke cikin fadamu.

Ya shawarci manoma da su mai da hankali sosai kan hasashen yanayi kafin su fara noman shinkafa, yana mai cewa gwamnatin tarayya na bayar da gargadin a farkon kowace kakar noma.

“Filayen da ke cikin ƙasa suna fama da takurewar girma, ƙarancin abinci mai gina jiki, da cututtukan fungal,” Onwe yayi gargaɗi.

Wata majiya daga ma’aikatar noma ta jihar Ebonyi da ta nemi a sakaya sunanta, ta tabbatar da cewa gwamnatin jihar na bin diddigin illolin da ambaliyar ruwa ta haifar a gonaki a halin yanzu.

Ya kara da cewa gwamnati na kuma tattara rahotanni daga yankunan da abin ya shafa domin daukar matakan da suka dace.

NAN ta ruwaito cewa hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMet), a hasashenta na yanayi, ta bayyana jihar Ebonyi a matsayin daya daga cikin jihohin da ake sa ran za su fuskanci ambaliyar ruwa a lokacin damuna ta 2025.

Jihar Ebonyi dai na daya daga cikin jihohin da ake noman shinkafa a Najeriya, kuma ‘yan kasuwar shinkafa a manyan kasuwannin Abakaliki, sun bayyana fargabar cewa farashin shinkafar na iya tashi sakamakon rashin girbi da ake sa ran za a samu. (NAN) (www.nannews.ng)

 

Edited by Aisha Ahmed

Kotu ta daure wani mutum saboda laifin satar tukunya

Hukunci

 

By Funmilayo Okunade

Ado-Ekiti, Aug. 6, 2025 (NAN) Wata kotun majistare dake Ado-Ekiti, ta yankewa wani matashi mai shekaru 33, Ige Bola, hukuncin zaman gidan yari na tsawon watanni biyu tare da aiki mai wahala bisa samunsa da laifin satar tukunyar da darajarsu ta kai N100,000.

Yayin hukuncin, a ranar Laraba, Alkalin kotun, Mista Bankole Oluwasanmi, ya yanke wa Bola hukunci ne bayan amsa laifinsa da kuma tabbatar da gaskiyar lamarin.

Dan sanda mai shigar da kara, Sifeto Elijah Adejare, ya shaidawa kotun cewa wanda ake tuhuma, ya aikata laifin ne a ranar 31 ga watan Yuli da misalin karfe 6:30 na yamma a Ilawe-Ekiti.

Adejare ya ce, wanda ake tuhumar ya saci tukwane guda uku da kudinsu ya kai N100,000 mallakar wani mutum mai suna Adenike Temiyemi.

Ya kara da cewa, wanda ake tuhumar a yanzu ya saci tukwanen ne a Ilawe-Ekiti ya kawo ta Ado-Ekiti, inda ya kara da cewa jami’an tsaro na Agro marshal sune suka kama shi.

Mai gabatar da karar yace an kama wanda ake tuhuma a lokacin da yake daukar tukwanen, daga bisani aka mika shi ga ‘yan sanda.

Ya kara da cewa ‘yan sanda sun kwato tukwanen kuma laifin ya ci karo da sashe na 302(1) (a) na dokar laifuka ta jihar Ekiti, 2021.(NAN)( www.nannews.ng )

FOA/DCO

Edited by Aisha Ahmed

Kotu ta daure wata mata yar shekaru 25, bisa zargin satar jariri dan watanni biyu

Daga Olawale Akinremi

Ibadan, Aug. 5, 2025 (NAN) Wata babbar kotun majistare da ke zamanta a Mapo, a Ibadan  ta bayar da umarnin tsare wata mata ‘yar shekara 25 mai suna Odunayo Odunlade, a gidan gyaran hali na Agodi, bisa zargin satar jariri dan watanni biyu.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN), ya ruwaito cewa Odunlade ta musanta zargin da aka yi mata, sai dai wanda ake zargin ba ta iya cika sharuddan belin da kotu ta yi mata ba.

Alkalin kotun, Mrs OO Latunji, ta bada belin Odunlade a kan kudi naira 500,000, tare da sa hannun wasu amintattun mutane guda biyu.

Daga bisani Latunji, ta dage zaman shari’ar zuwa ranar 21 ga watan Oktoba, domin yi kammala shari’ar.

Lauya mai shigar da kara, Insp. Oluseye Akinola, ya shaida wa kotun cewa, wadda ake tuhuma ta aikata laifin ne a ranar 24 ga watan Yuli, a unguwar Lascap-Oniyanrin da ke Ibadan.

Akinola ya ce, Odunlada saci yaron ne daga dakin da mahaifiyarsa ta ajiye shi, ya kara da cewa jami’an ‘yan sanda a ofishinsu na Mokola, sun kai daukin gaggawa bayan sun samu bayanai kan ta’asar.

Jami’in ya tabbatar da cewa ‘yan sanda sun yi nasarar bin diddigin wadda ake kara, a wani wurin da bai bayyana ba, kwanaki kadan bayan sace yaron.

A cewar sa, laifin da matar da ake zargi ta aikata, ya ci karo da tanadin sashe na 390(9) na kundin laifuffuka, Cap. 38, Vol. ii, Dokar Jihar Oyo, 2000. (NAN)

Edited by Aisha Ahmed

 

Annoba a Neja: Matar Tinubu ta ba da gudummawar N1bn ga wadanda abin ya shafa

 

Daga Celine-Damilola Oyewole

Ambaliya

Minna, 5 ga Agusta, 2025 (NAN) Matar shugaban kasa, Sen. Oluremi Tinubu ta ba da gudummawar Naira biliyan daya don tallafawa mutanen da annoba ta shafa a fadin jihar Neja.

Tinubu, ta bayar da wannan tallafin ta hanyar aikin da ta kirkiro na Renewed Hope Initiative (RHI) a ranar Talata a Minna, ta ce wadanda za su ci gajiyar su ne wadanda ambaliyar ruwa, gobara, da hatsarin kwale-kwale da wadanda harin ‘yan fashi ya shafa.

Ta bayyana annoba a matsayin abin dubawa, inda ta ce, hakika wadannan lokuta ne masu wahala, ta kuma yi adduar Allah ya jikan wadanda suka rasu, tare da ba marasa lafiya wadanda suka jikkata Lafiya.

Uwargidan ta kuma amince da sa hannun gwamnatin tarayya cikin gaggawa, wajen raba kudade da kayayyakin agaji ga wadanda abin ya shafa.

Bugu da kari ta yi nuni da cewa, tausayi yana inganta al’umma ya na kuma kara mata jajircewa a lokutan wahala, inda ta kara da cewa, ya kamata mutane su koyi tausayawa juna.

“Na yi farin ciki da cewa Shugaba Bola Tinubu, ya amince da gaggauta a saki kudade da kayayyakin abinci don taimakawa wajen farfado da gine-ginen da ambaliyar ruwa ta lalata.

“Na zo nan ne domin in jajanta wa Gwamna Mohammed Bago, da al’ummar Jihar Neja, kan mumunar ambaliyar ruwa da ta addabi karamar hukumar Mokwa, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.

“Ina kuma yabawa kokarin gwamnan, na tashi tsaye wajen aiki tare da bayar da gudummawar kudade da abinci, domin tallafawa iyalan da suka rasa matsugunansu.

“Don tallafawa kokarin sake gina jihar Neja, majalisar gudanarwar kungiyar Renewed Hope Initiative, ta bayar da gudummawar Naira biliyan daya, tare da kayayyakin agaji.

“Kayayyakin sun hada da tufafi, takalma, da buhunan shinkafa 50,000 ga jihar ta Neja,” inji Uwargidan shugaban kasa Tinubu.

Mai dakin shugaban Kasar ta kuma jajantawa wadanda hatsarin kwale-kwale ya rutsa da su, da wadanda harin ‘yan bindiga ya rutsa da su, kana da wadanda suka ibtila’in gobara a jihar.

“A matsayina na uwa, na yi imanin cewa dukkanmu za mu iya shawo kan wannan bala’i tare da taimakawa al’umma ta wartsake. Allah ya baku lafiya, ya kuma jikan wadanda suka rasu.

“Za a yi amfani da kudaden wajen bada tallafin gidaje da muhimman kayayyaki, don a taimakawa iyalan wadanda suka rasa matsugunansu domin su dawo kan kafafunsu,” Uwargidan ta ce.

Haka kuma, ta jaddada cewa wannan ya yi daidai da manufar shirin nata, kamar yadda yake kunshe a taken su “Ingantacciyar Rayuwa zuwa ga Iyalai”.

Kamfanin Dillancin labarai na kasa (NAN), ya ruwaito cewa, gwamnan Neja, Umar Bago, ya yabawa shugaba Tinubu da matarsa bisa goyon bayan da suke baiwa jama’a. (NAN) (www.nannews.ng)

Edited by Aisha Ahmed