Maniyyata aikin Hajji guda 2 sun rasu a hatsarin mota a Kano — Hukuma

Maniyyata aikin Hajji guda 2 sun rasu a hatsarin mota a Kano — Hukuma

Spread the love

Maniyyata aikin Hajji guda 2 sun rasu a hatsarin mota a Kano — Hukuma

Maniyyata
Daga Bosede Olufunmi
Kano, Afrilu 23, 2026 (NAN) Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano ta sanar da rasuwar maniyyata aikin Hajjin bana guda biyu a hatsarin mota da ya faru a Rimin Gado da ke Kano.

Wannan yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar, Sulaiman Dederi ya fitar a Kano.

A cewar sanarwar, sunayen mamatan kamar haka: Alkasim Ibrahim-Walawa, mai shekaru 48, da mahaifiyarsa, Hadiza Garba, mai shekaru 73, an ce suna tafiya ne don shirin zuwa aikin Hajji lokacin da hatsarin ya faru.

Ya ce “dukkan wadanda abin ya shafa ‘yan asalin kauyen Walawa ne a karamar Hukumar Kabo ta Jihar Kano.”

Dederi ya ce rasuwarsu abin tausayi ne musamman domin suna kan tafiya mai daraja da nufin zuwa kasa mai tsarki don aikin Hajji.

Hukumar ta mika ta’aziyya ga iyalan da suka rasu tare da addu’ar Allah ya ba su ƙarfi da haƙuri don jure rashin.(NAN)(www.nannews.ng)
BO/YMU
=========
Yakubu Uba ne ya gyara


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *