Kotun Shari’ah ta umarci tsohon miji da ya kara kudin abincin yara
Kotu Shari’ah ta umarci tsohon miji da ya kara kudin abincin yara
Kaduna, 15 Yuli, 2026 (NAN) Kotun Shari’a da ke zaune a Magajin Gari, Jihar Kaduna a ranar Laraba ta umarci Malam Nasiru da ya kara kudin abincin yau da kullum ga yaransa biyu daga N2,000 zuwa N3,000.
Kotun ta kuma umarci Nasiru da ya biya kudin haya na gidan su.
Wannan umarni ya biyo bayan karar da tsohuwar matarsa, Maimuna Gambo, ta shigar domin neman karin kudin abincin yaran su.
Gambo ta shaida wa kotu cewa sun rabu a ranar 28 ga Yuni, kuma ‘ya’yansu biyu, masu shekaru hudu da daya, suna tare da ita a gidan da wanda ake kara ya haya kafin saki.
Ta kara da cewa tana da ciki na watanni shida kuma Nasiru yana bayar da N2,000 kawai a kullum don abinci, ba tare da hada da kayan sawa, kudin asibiti, kudin makaranta da sauran abubuwan bukatu ba.
“Ba ya isa na ciyar da ni da yaran sa biyu a rana. Ina rokon kotu ta tilasta masa ya karawa yara kudin abinci kuma ya dauki nauyin yaran da ciki,” in ji ta.
Sai dai, Nasiru ya shaida wa kotu cewa shi direban babur ne na kasuwanci kuma kawai zai iya biyan kudin da yake biya, amma yana son kara N500.
Mai kara ya ki yarda da karin kudin da aka bayar.
A cikin hukuncinsa, Alkalin, Malam Yakubu Abdullahi, ya umarci Nasiru da ya rika biyan N3,000 a rana don ciyar da yaran, kuma ya umurce shi
da ya biya kudin haya. (NAN)(www.nannews.ng)
HMG/WS
========
Wandoo Sombo ce ta gyara

