Yusuf ya sanarwa masu rike da mukamai da ke son tsayawa zaben 2027 da su yi murabus
Yusuf ya sanarwa masu rike da mukamai da ke son tsayawa zaben 2027 da su yi murabus
Zaɓe
Daga Aminu Garko
Kano, Maris 25, 2026 (NAN) Gwamna Abba Yusuf na Jihar Kano ya umurci wadanda ke rike da mukamai wadanda ke da sha’awar tsayawa takara a zaben 2027 da su yi murabus, don daidaito da Dokar Zabe.
Umarnin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakinsa Sanusi Dawakin-Tofa ya fitar a Kano ranar Laraba.
Sanarwar ta ce dole ne masu sha’awar su yi murabus kafin ranar 31 ga Maris, 2026, domin tabbatar da daidaito da dokar zabe.
An bayar da umarnin ne ta hanyar wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Umar Ibrahim ya fitar, inda ya jaddada bukatar bin dokokin da suka shafi jami’an gwamnati.
Sanarwar ta bayyana cewa wannan hukunci ya yi daidai da Sashe na 88 (1) na Dokar Zaɓe ta 2026, wanda ke tsara shigar masu riƙe da mukamai a harkokin siyasa na jam’iyya.
Ta ƙara da cewa an yi wannan matakin ne don tabbatar da riƙon amana, da kuma mutunci a cikin ayyukan gwamnati, tare da tabbatar da daidaito ga dukkan masu neman takara.
A bisa ga da’irar, ana buƙatar waɗanda aka naɗa a siyasa waɗanda ke da niyyar tsayawa takara a zaɓe mai zuwa su yi murabus ko su yi ritaya, kamar yadda ya dace, a ranar ko kafin Talata, 31 ga Maris, 2026.
Ta kuma umurci dukkan Ma’aikatu da Hukumomi da su bai wa wannan sanarwa cikakken goyon bayar tare da tabbatar da cewa an bi dukkan ka’idojin da suka dace. (NAN) ( www.nannews.ng )
AAG / IEI / EAL
==================
Edited by Ijendu Iheaka/Ekemini Ladejobi

