Tinubu zai halartarci taron koli na Saint Lucia, BRICS a Brazil
Tinubu zai halartarci taron koli na Saint Lucia, BRICS a Brazil
Ziyarci
By Muhydeen Jimoh
Abuja, Yuni 28, 2025 (NAN) Shugaban kasa Bola Tinubu ya bar Abuja domin ziyarar kasashe biyu a Saint Lucia da Brazil.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Mista Bayo Onanuga, ya fitar ranar Juma’a a Abuja.
Onanuga ya ce, ziyarar farko da shugaba Tinubu zai kai shi ne Saint Lucia domin ziyarar aiki da nufin karfafa alaka da kasashen Caribbean da kuma bunkasa hadin gwiwar Kudu-maso-Kudu.
Bayan ziyarar, shugaban zai tafi Brazil don halartar taron BRICS karo na 17 a Rio de Janeiro.
Onanuga ya ce yayin da yake Saint Lucia, Tinubu zai kai ziyarar ban girma ga Gwamna-Janar, Cyril Errol Melchiades Charles da Firayim Minista Philip Pierre.
Ya ce babban abin da ya fi daukar hankali a ziyarar shi ne jawabin da zai yi a wani zama na musamman na hadin gwiwa na Majalisar Dattawa da ta Saint Lucian.
Onanuga ya ce Tinubu zai kuma halarci wani babban taron cin abincin rana tare da shugabannin gwamnatocin kungiyar kasashen gabashin Caribbean (OECS).
Taron cin abincin rana zai duba hanyoyin zurfafa hadin gwiwar Najeriya da OECS a fannin tattalin arziki da hadin kan al’adu.
An kuma shirya zai ziyarci Kwalejin Al’umma ta Sir Arthur Lewis a Castries don haɓaka musayar ilimi da haɗin gwiwar ilimi.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Najeriya da Saint Lucia na ci gaba da kulla alaka ta Majalisar Dinkin Duniya da Commonwealth, tare da raba gadon Afirka da moriyar juna.
Ziyarar na da nufin bude hanyoyin samar da ababen more rayuwa, ilimi, ci gaban matasa, da hadin gwiwar diflomasiyya.
Onanuga ya ce bayan ganawar sa a Saint Lucia, Tinubu zai tafi Brazil don halartar taron BRICS daga ranar 6 zuwa 7 ga watan Yuli.
Zai halarci taron ne bisa gayyatar da shugaban kasar Brazil Lula da Silva ya yi masa, inda ya amince da Najeriya a matsayin ‘kasa aminiyar BRICS’.
NAN ta ba da rahoton cewa taron na BRICS karo na 17 yana da takensa: “Ƙarfafa haɗin gwiwar Kudancin Duniya don Ingantacciyar Mulki da Dorewa.”
Tattaunawar za ta mayar da hankali ne kan fadada hadin gwiwa a fannin zamantakewa, tattalin arziki, da kuma muhalli a fadin Kudancin Duniya.
Onanuga ya ce manyan jami’an gwamnati za su raka shugaba Tinubu a ziyarar biyu. (NAN) (www.nannews.ng)
MUYI/CHOM
==========
Chioma Ugboma ta gyara