Mataimakin shugaban majalisar dattawa ya goyi bayan kirkiro jihar Karaduwa

Mataimakin shugaban majalisar dattawa ya goyi bayan kirkiro jihar Karaduwa

Spread the love

Mataimakin shugaban majalisar dattawa ya goyi bayan kirkiro jihar Karaduwa

Jiha

Daga Abbas Bamalli da Naomi Sharang

Funtua (Jihar Katsina) 1 ga Maris, 2025 (NAN) Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Jibrin Barau, ya nuna goyon bayansa ga kirkiro da Jihar Karaduwa daga Jihar Katsina.

Ya bayyana haka ne a garin Funtuwa ta jihar Katsina a lokacin rabon kayan abinci na watan Ramadan wanda Sanata Muntari Dandutse mai wakiltar mazabar Katsina ta Kudu ya shirya.

Barau wanda shi ne shugaban kwamitin majalisar dattawa kan duba kundin tsarin mulkin ya bayyana irin karfin noma da shiyyar ke da shi, ya kuma tabbatar da cewa ta cancanci samun jiharta.

Ya kuma ba da tabbacin cewa zai yi duk mai yiwuwa domin ganin al’umma su cimma burinsu na samar da jihar Karaduwa.

“Kira kan kirkirar Jihar Karaduwa, ta dace kuma manufa ce mai kyau; kyakkyawan fata ne daga mutanen Karaduwa.

“Wannan yanki ne na noma. Suna da duk abin da ake bukata don samun jiha. Amma kun san ka’idojin tsarin mulki don samun jiha. Ina tare da ra’ayoyinsu. Ina goyon bayansu.

“Zan yi duk mai yiwuwa. Kar ku manta, makwabtana ne mu da yankin Majalisar dattawa da na ke wakilta, muna iyaka da wannan yanki, don haka na san abin da suke bukata.”

Dandutse, a yayin taron, ya zayyana kayayyakin da aka tanada domin karfafawa mutane, wadanda suka hada da shinkafar da baza ta gaza tireloli takwas ba.

Ya kuma raba buhunan taki guda 5,439, buhunan masara 3,795, injinan dinki 384, da injinan nika 110 domin tallafa wa mazabun a cikin watan Ramadan.

Shima da yake jawabi a wajen taron, mataimakin shugaban jam’iyyar APC na jihar, Alhaji Bala Abu-Musawa, ya yi kira ga majalisar dokokin kasar da ta samar da jihar Karaduwa.

Ya yabawa Dandutse bisa goyon bayan da yake bayarwa wajen bayar da shawarwarin kafa Jami’ar Kimiyyar Kiwon Lafiya ta Tarayya a Karamar Hukumar Funtua.(NAN)(www,nannews.ng)

AABS/NNL/ISHO/AMM

================

Yinusa Ishola da Abiemwense Moru ne suka shirya


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *