Ƙungiyar haɗin gwiwa ta yi kira da a saka hannun jari a ilimin ‘yan mata don kawo ƙarshen auren kanan yara

Ƙungiyar haɗin gwiwa ta yi kira da a saka hannun jari a ilimin ‘yan mata don kawo ƙarshen auren kanan yara

Spread the love

​⁠⁠⁠‍​⁠‍⁠Aure

Daga Ibrahim Shehu

Sokoto, Oktoba 12, 2026 ( NAN ) Hadakar kungiyoyin sa kai a Jihar Sokoto, sun yi kira ga gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki, da su kara zuba jari a fannin ilimin ‘yan mata domin dakile auren wuri.

Shugaban Ƙungiyar hadakar na jihar, Dakta Hassan Ibn-Attahir, ya yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, don tunawa da Ranar Yara Mata ta Duniya ta 2026 a Sakkwato.

Bikin na tunawa da ranar, mai taken ‘Ilmantar da mata a Yau, Kawo Karshen Auren Yara Gobe’, ya nuna rawar da ilimi ke takawa wajen kare hakkokin ‘yan mata da kuma hana auren wuri ga yara ƙanana

Ibn-Attahir ya ce, ci gaba da ‘yan mata ke samu a makaranta yana da matukar muhimmanci wajen kawo karshen auren yara ƙanana, yana mai ƙara da cewa ilimi yana ƙarfafa su, su yanke shawara mai ma’ana da kuma ba da gudummawa mai ma’ana ga al’umma.

“Kawo karshen auren yara kanana ba abu ne da ba za a iya raba shi da barin ‘yan mata su yi makaranta ba.

“Yarinya mai ilimi za ta zama mace mai ƙarfi wadda za ta gina al’ummomi masu ƙarfi da kuma samar da makoma mai haske ga Jihar Sakkwato,” in ji shi.

Ya yi kira ga gwamnatin jihar, cibiyoyin gargajiya da na addini, iyaye, abokan hulɗa na ci gaba, da sauran masu ruwa da tsaki, da su ba da fifiko ga ilimin ‘yan mata, a matsayin wata hanya mai mahimmanci ta kawo ƙarshen auren wuri.

A cewarsa, ingantaccen ilimi yana haɓaka ci gaban mutum, lafiya da walwala, haɓaka ƙwarewa, kirkire-kirkire, da samar da ‘yancin tattalin arziki, yayin da yake ba da gudummawa ga al’ummomi wajen zaman lafiya.

Ibn-Attahir ya ce ƙungiyar, ta tsara ayyukan da za su yi don bikin ranar, ciki har da kamfen ɗin wayar da kan makarantu, shirin tattaunawa ta rediyo, ziyarar sada zumunci tsakanin masu ruwa da tsaki, da kuma wani kamfen na kafofin sada zumunta na jihar baki ɗaya.

Ya sake jaddada alƙawarin haɗin gwiwar, na tabbatar da cewa kowace yarinya a Jihar Sakkwato, ta sami damar samun ilimi, kariya da kuma damar cimma cikakkiyar damarta.

Ana bikin ranar yaran mata ta duniya kowace shekara a ranar 11 ga Oktoba, domin nuna haƙƙoƙin ‘yan mata da ƙalubalen da suke fuskanta a duniya. (NAN )

 

IBST/KTO

Fassarar Aisha Ahmed

=============

Edita daga Kamal Tayo Oropo


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *