Matata na dauke da cikin wani na miji, mai neman saki ya fada wa kotu
Matata na dauke da cikin wani na miji, mai neman saki ya fada wa kotu
Saki
Daga Patience Yakubu
Kaduna, Maris 13, 2025 (NAN) A ranar Alhamis ne wani dan kasuwa mai shekaru 49, Richard Julius, ya
bukaci wata kotun gargajiya da ke Kaduna ta raba aurensa da matarsa Jemimah na tsawon shekaru 12, saboda zargin zina da rashin mutuntawa.
Mai shigar da karar, mazaunin Barnawa a cikin birnin Kaduna, ya yi zargin cewa wani mutum ne matarsa ta dauki ciki
yayin da yake zaune a gidansa.
A cewarsa, matarsa ta yaudare shi da maza da dama a tsawon shekaru 11 da aurensu wanda suka haifi ‘ya’ya 4.
Yace “ina son wannan kotu mai daraja ta raba auren nan saboda matata ta raina ni ta hanyar yaudarata da maza
daban-daban wadanda ba ta boyewa.
“A halin yanzu, tana da ciki ga wani mutum, kuma ba zan iya karɓar ɗan wani ba yayin da nake da ‘ya’ya hudu don ciyarwa da reno.”
Julius ya kara kokawa kan halin matarsa na rashin kwana a gidan aurensu.
Ya shaida wa kotun cewa a wani lokaci, ta shafe tsawon mako guda tana mai cewa ta ziyarci kauyene, amma da ya tunkareta, sai ta yarda ta je ganin mazajen da take ganin sun fi shi ne, sai tace masa idan bai ji dadin hakan ba to ya sake ta.
“Hakan ya jawo cece-kuce a tsakaninmu tsawon shekaru, wasu watannin da suka gabata mun je ganin limamin cocinmu kan lamarin,
kuma ta yi alkawarin canjawa amma ta ki.
“Na sha rokon ta saboda yara, don mu rayu cikin farin ciki amma ba ta son hakan. Abin da nake so shi ne kotu ta raba auren nan ta kuma ba ni rikon ‘ya’yana.”
Amma wacce ake kara ta musanta zargin da mijinta ya yi mata, sai ta bukaci kotu da ta amince da bukatar mijin nata na raba auren.
Tace “ina da ciki amma hakan ba yana nufin ba shi ne uba ba domin ba na kwana da wani namiji.
“Nima ina son a raba auren nan saboda na gaji da rigima da zargin da ake yi a kullum.”
Alkalin kotun, John Dauda, ya shawarci ma’auratan da su wanzar da zaman lafiya sannan ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 28 ga watan Afrilu.(NAN)(www.nannews.ng)
PMY/KO
=======
Kevin Okunzuwa ne ya gyara