Kotu ta tsare wani mutum bisa zarginsa da lalata da yarinya ‘yar shekara 8
Kotu ta tsare wani mutum bisa zarginsa da lalata da yarinya ‘yar shekara 8
Lalata
Daga Raji Rasak
Badagry (Jihar Legas), Afrilu 25, 2025 (NAN) Wata Kotun Majistare ta Badagry da ke zamanta a Legas, a ranar Larabar da ta gabata ta tasa keyar wani matashi mai shekaru 23, Mautin Odun a gidan yari bisa zarginsa da lalata wata yarinya ‘yar shekara takwas.
Alkalin kotun, Patrick Adekomaiya, ya bayar da umarnin a tsare Odu a gidan yari na Awarjigoh, Badagry, bayan ya ki amsa laifinsa na lalata
da kuma tabawa ba bisa ka’ida ba.
Ya ba da umarnin a kwafi fayil din a aika zuwa ofishin daraktan kararrakin jama’a (DPP) don neman shawarar lauya.
Adekomaiya ya dage sauraron karar har zuwa ranar 3 ga watan Yuni, domin yanke hukunci kan neman belin da kuma shawarar shari’a ta DPP.
Tun da farko, dan sanda mai shigar da kara, Ayodele Adeosun, ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifin ne a ranar 23 ga
Afrilu, da karfe 3 na rana, a gidan Sikiru, Tozunkanmeh, Ajara, Badagry, Legas.
Mai gabatar da kara ya ce laifin ya ci karo da tanadin sashe na 261 da 263 na dokar laifuka ta jihar Legas, 2015. (NAN) (www.nannews.ng)
ROR/SH
=======
Sadiya Hamza ce ta gyara