Jami’in yi ma kasa hidima ya gyara ajujuwan makaranta 2 a Jigawa

Jami’in yi ma kasa hidima ya gyara ajujuwan makaranta 2 a Jigawa

Spread the love

Jami’in yi ma kasa hidima ya gyara ajujuwan makaranta 2 a Jigawa

Gyarawa

Daga Muhammad Nasiru Bashir

Dutse, Maris 14, 2025 (NAN) Wata ‘yar mai yiwa kasa hidima (NYSC) a Jigawa, Miss Banigbe Onyilola, ta gyara wani katanga na ajujuwa biyu a makarantar karamar sakandare ta gwamnati da ke a karamar hukumar Dutse.

Da take gabatar da aikin ga hukumomin makarantar a ranar Juma’a, Onyilola ta ce hakan na daga cikin shirinta na ci gaban al’umma (CDS) na makarantar kafin ficewarta daga shirin yi wa kasa hidima.

Ta bayyana cewa, tun bayan da ta je makarantar, ta lura da yadda ajujuwan biyu suka lalace da kuma karyewar  kayan aikin dalibai.

“Wadannan azuzuwan ba su da kyau, babu daben kasa, babu sili, babu kayan daki. Don haka kamar yadda kuke gani na gyara su, ciki har da matakalar bene, silin da fenti.

” Na gyara wa dalibai kusan tebura da kujeru 20. Wannan shi ne don sanya koyo ga ɗalibai cikin sauƙi da jin daɗi,” in ji ta.

‘ Jam’i’ar ta bayyana cewa ta gudanar da ayyukan ne a matsayin gudunmawar da take baiwa al’ummar da ta karbi bakuncin ta, jihar da kuma Najeriya baki daya.

A cewarta, an gudanar da ayyukan ne tare da tallafi daga karamar hukumar Dutse, ofishin shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar Jigawa, ofishin hukumar tattara kudaden shiga na jihar Jigawa, ofishin kakakin majalisar dokokin jihar Jigawa.

Ma’aikatar Harajin Cikin Gida ta Tarayya, ofishin Jahar Jigawa, ofishin shugaban ma’aikata,sakataren gwamnatin jiha, akanta janar, kwamishinan ma’aikatar kananan hukumomi da ofishin mai binciken kudi.

Sauran sun hada da Sakatare na dindindin, Ma’aikatar Ilimi, Babban Sakatare a Ma’aikatar Muhalli da Kodinetan Jiha na ayyukan PLANE a jihar, da dai sauransu.

Da yake tsokaci, kodinetan NYSC a jihar, Malam Jidda Dawut, ya yabawa jam’i’ar tare da yin kira ga sauran masu yiwa kasa hidima da su yi koyi da wannan matakin.

Dawut ya kuma yi kira ga ’yan uwa da su rika tallafa wa ’yan kungiyar don gudanar da ayyuka a cikin al’ummarsu ta hanyar amincewa da daukar nauyinsu.

Tun da farko, shugaban makarantar Malam Ali Jibril, ya yabawa Onyilola bisa wannan karimcin da hukumar ta NYSC da ta kasance hanyar samar da ma’aikata ga makarantu da dama a jihar.

“Na yi shirin gyara ajujuwan biyu tun shekaru shida da suka gabata, ga mu yau, wani dan kasa nagari ya yi mana haka.

Shugaban makarantar ya ce “Mun yaba da kokarinta kuma muna kira ga sauran masu aiki a sassan jihar da su yi koyi da ita.”

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa Onyilola ta kuma dasa itatuwa 50 a kusa da makarantar da sauran al’ummomin da ke kusa da makarantar. (NAN) (www.nannews.ng)

Joe Idika ya gyara MNB/JI


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *