Hukumar NAFDAC ta gargadi masu sayar da ‘ya’yan itatuwa da su guji amfani da sinadari mai cutarwa
Hukumar NAFDAC ta gargadi masu sayar da ‘ya’yan itatuwa da su guji amfani da sinadari mai cutarwa
‘Ya’yan itace
Daga Ibrahim Kado
Yola, Fabrairu 27, 2025 (NAN) Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) a Adamawa ta gargadi masu sayar da ’ya’yan itace da su guji amfani da sinadarin masu cutarwa wajen nunar da ’ya’yan itatuwa, ta kuma shawarci masu amfani da su su yi hattara.
Mista Gonzuk Bedima, Jami’in NAFDAC a Adamawa, ya yi wannan gargadin ne a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Yola ranar Alhamis.
Ya kara da cewa, sinadarin mai hadari da aka fi amfani da shi wajen sa ‘ya’yan itatuwa su nuna, musamman ayaba da lemu, shi ne sinadarin calcium carbide, wanda ake amfani da shi wajen yin walda.
A cewar Bedima, wannan sinadari na iya haifar da cutar daji a kowane bangare na jiki.
Ya kara da cewa, a baya hukumar NAFDAC ta wayar da kan shugabannin masu sayar da ‘ya’yan itace da kuma
shirin ci gaba da gudanar da wannan gangamin, musamman ganin yadda lokacin azumi ya gabato, inda mutane da
dama ke siyan kayan marmari a gidajensu.
Jami’in ya bukaci masu amfani da su da su kasance masu taka-tsan-tsan kuma su guji sayen ‘ya’yan itatuwa da aka nuka da sinadarai saboda illar da ke tattare da lafiyarsu.
Ya bayyana cewa ‘ya’yan itatuwa da aka sa musu maganin calcium carbide sukan bayyana sun nuna sosai a waje amma ba
a ciki ba.
Yace “idan kuna zargin irin wadannan ‘ya’yan itatuwa, to ku guji siyan su, domin suna da hadari ga lafiyar ku,” inda ya bukaci jama’a su kai rahoto ga hukumar NAFDAC domin a doki matakin da ta dace. (NAN)(www.nannews.ng)
IMK/FNO/AMM
============
Franca Ofili da Abiemwense Moru ne suka gyara