‘Yan majalisa sun koka kan rashin tsaro a Nasarawa
Tsaro
By Awayi Kuje
Lafia, Aug. 22, 2025 (NAN) Majalisar Dokokin jihar Nasarawa, ta ja hankulan jama’a game da karuwar matsalar rashin tsaro a jihar, musamman masu garkuwa da mutane.
Dokta Danladi Jatau, kakakin majalisar ne ya bayyana hakan a bayan da dan majalisar da ke wakiltar mazabar Lafia ta tsakiya, Mista Solomon Akwashiki, ya tabo batun.
Akwashiki, ya tabo batun da ya shafi bukatun jama’a a domin jaddada zaman majalisar a Lafiya.
Shugaban majalisar ya yi kira ga hukumomin tsaro a jihar, da su yi amfani da dokar yaki da garkuwa da mutane da majalisar ta kafa domin dakile satar mutane a jihar.
Ya kuma nuna damuwarsa kan yadda ake hada baki da masu satar mutane a yi garkuwa da mutane, yana mai nuna damuwa cewa jihar na zama cibiyar garkuwa da mutane.
“Kudirinmu na haka ne, muna kira ga gwamnan jihar, da ya umarci jami’an tsaro su kara karfafa tsaro a fadin jihar.
“Na biyu, muna umurtar jami’an tsaro da su yi amfani da dokar da wannan majalisa ta kafa, wajen dakile garkuwa da mutane.
“Na uku, muna kira ga mazauna yankin da su kai rahoton duk wani motsi da ayyukan daidaikun mutane ga jami’an tsaro, don daukar mataki,” in ji kakakin.
Tun da farko, Mista Akwashiki, mamba mai wakiltar mazabar Lafia ta tsakiya, ya nuna damuwa akan cewa Lafia, babban birnin jihar Nasarawa ba shi da mafaka, sakamakon ci gaba da yin garkuwa da mutane.
“Mai girma shugaban majalisar, idan Lafia ba ta da lafiya ina kuma za a samu lafiya?
“Wadannan masu garkuwa da mutane suna ta kai hare-hare, suna barna ba tare da wata tangarda ba, dole ne mu tashi kafin lokaci ya kure,” in ji Akwashiki.
Shima da yake bayar da gudunmawarsa, Daniel Ogazi (APC-Kokona Gabas) ya tunatar da majalisar cewa majalisar dokokin jihar ta zartar da dokar yaki da garkuwa da mutane.
“Dokar da wannan majalisa ta kafa ta tanadi cewa idan aka kama mai garkuwa da mutane, a kawar da shi ko ita, wannan yana aiki, amma ba mu san abin da ya faru daga baya ba,” in ji Ogazi.
Da suke bayar da gudunmawa, shugaban masu rinjaye na majalisar, Mista Suleiman Azara, Mista Esson Mairiga (PDP-Lafia North) da kuma Mista Mohammed Omadefu (APC-Keana), sun bukaci hukumomin tsaro da su canza salon dakile satar mutane. (NAN) (www.nannews.ng)
AKW/BEKl/COF
Fassarar Aisha Ahmed