Sojojin Guinea-Bissau sun ayyana Janar a matsayin Shugaban sabon mulkin soja a kasar
Gabaɗaya
Dakar, 28 ga Nuwamba, 2025 (dpa/NAN) A ranar Alhamis ne sojojin kasar Guinea-Bissau da ke gabar tekun yammacin Afirka, suka sanar da nada sabon shugaba.
Gidan yada labarai na gwamnati TGB, ya ruwaito cewa Janar Horta Inta-A, zai yi aiki a matsayin shugaban rikon kwarya na tsawon shekara guda.
Ya zuwa yanzu dai, ba a fayyace komai game da daidaiton madafun iko a kasar da kuma yanayin da ake zargin juyin mulkin, kwanaki kadan bayan zaben shugaban kasar zai haifar ba.
Shaidun gani da ido sun shaidawa dpa cewa, titunan babban birnin kasar, Bissau, ba kowa, yayin da aka jibge sojoji a muhimman wurare a fadin birnin.
Kwana daya da ta gabata, wasu gungun jami’ai sun ce sun karbi mulki a kasar mai dauke da mutane kusan miliyan 2.2.
Sun ce sojoji sun bankado wani shiri na magudin zabe da kuma tada zaune tsaye a kasar, wanda ya hada da ‘yan siyasa da masu safarar miyagun kwayoyi.
Guinea-Bissau dai muhimmiyar cibiyar safarar hodar Iblis ce tsakanin Latin Amurka da Turai.
Rahotanni sun ce, shugaba Umaro Sissoco Embaló da aka hambare a yanzu, ya shaidawa kafar yada labaran Faransa cewa sojoji sun tsare shi. Sai dai ya ce ba a yi masa lahani ba.
An kuma ce sojoji sun tsare abokin hamayyar Embaló, Fernando Dias.
Duka Embaló da Dias, sun bayyana kansu a matsayin wadanda suka yi nasara bayan zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar Lahadi. Har yanzu ba a buga sakamakon zaben ba.
Kasar Guinea-Bissau dai ta fuskanci juyin mulki da yunkurin juyin mulki da dama tun bayan samun ‘yancin kai daga kasar Portugal a shekarar 1974.
Sojoji sun shafe shekaru da dama suna shiga siyasa sosai.
Tsohon Janar Embaló yana kan karagar mulki tun shekarar 2020, kuma ya rusa majalisar a karshen shekarar 2023.
A baya dai ya sha yin magana game da yunkurin juyin mulkin da aka yi masa, na baya bayan nan a watan Oktoba.
HS
===
Halima Sheji ta gyara
AAA/
Aisha Ahmed ta fassara

