Skip to content

Search news

Type to search stories, topics and pages.

Latest
Uncategorized

Cika Shekaru 20: MMPN ta yabawa gudummawar Sultan ga hadin kan kasa

By 2 min read

Cika Shekaru 20: MMPN ta yabawa gudummawar Sultan ga hadin kan kasa

Sultan

Na Ibrahim​​​​​​​​​​​​​​ Shehu​​​​​​​​​

Sokoto, Nuwamba 1, 2026 (NAN) Kungiyar Muslim Media Practitioners of Nigeria (MMPN) ta yabawa mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, bisa gudunmawar da yake bayarwa ga Musulunci, dan Adam da hadin kan kasa.

Shugaban MMPN na ƙasa, Alhaji Abdurrahman Balogun, ya yi wannan yabo a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi don taya Sarkin Musulmi murnar cika shekaru 20 da nada shi.

Balogun ya bayyana wannan muhimmin ci gaba a matsayin shekaru ashirin na hidima mai ban mamaki ga Musulunci, Al’ummar Musulmi da Najeriya, wanda aka siffanta shi da mutunci, hikima da kuma sadaukar da kai ga zaman lafiya da haɗin kai.

Ya ce Sarkin Musulmi, wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), ya  na da matsayi na musamman a cikin kungiyar a matsayin Ban for a Kasa

Shugaban ya yaba da goyon bayan da Sarkin Musulmi ke bai wa masu aikin yada labarai na Musulunci da kuma yadda kafafen yada labarai ke taka rawa wajen inganta fahimta, zama dan kasa mai alhaki da kuma zaman lafiya.

A cewarsa, Sarkin Musulmi, tsawon shekaru, ya yi amfani da matsayinsa wajen inganta tattaunawa, haƙuri da girmama juna tsakanin ‘yan Najeriya masu addinai da asali daban-daban.

“A lokacin da ƙasar ke fuskantar mawuyacin hali, waɗannan saƙonnin sau da yawa suna ba mu tabbaci kuma suna tunatar da mu abubuwan da ke haɗa mu wuri ɗaya,” in ji shi.

Balogun ya ce ƙarfafa gwiwar Sultan ya ƙarfafa ƙudurin masu aikin watsa labarai na Musulmi na sauke nauyin da ke kansu na aiki da adalci, ƙwarewa da kuma jin cewa suna da alhakin jama’a.

Ya ce MMPN ta haɗu da al’ummar Musulmi, Majalisar Sarauta, al’ummar Sakkwato da kuma ‘yan Najeriya a faɗin ƙasar wajen murnar wannan muhimmin ci gaba.

Shugaban MMPN ya yi addu’ar Allah Madaukakin Sarki ya ci gaba da ba Sarkin lafiya, hikima da ƙarfi don ƙarin shekaru na hidima ga Musulunci, ɗan adam da Najeriya.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Sarkin ya hau karagar mulki a ranar 2 ga Nuwamba, 2006, bayan amincewar masu naɗa sarki, inda ya gaji babban ɗan’uwansa, Sultan Muhammadu Maccido.

Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *