UNICEF, masu ruwa da tsaki a harkar kiwon lafiya na neman ingantattun kudade don kula da lafiyar mata da yara

UNICEF, masu ruwa da tsaki a harkar kiwon lafiya na neman ingantattun kudade don kula da lafiyar mata da yara

Spread the love

UNICEF, masu ruwa da tsaki a harkar kiwon lafiya na neman ingantattun kudade don kula da lafiyar mata da yara

Tallafin Kudi
Daga Folasade Akpan
Abuja, 4 ga Yuni, 2025 (NAN) Masu ruwa da tsaki a harkar lafiya sun sake sabunta kiraye-kirayen a kara yawan kasafin kudin inganta da kula da lafiyar mata da yara a kasar nan.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya rawaito cewa masu ruwa da tsakin sun yi wannan kiran ne a wani taron karawa juna sani da kungiyar ci gaban kasa da kasa wato Debelopment Governance International (DGI) Consult ta shirya tare da tallafin asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF a ranar Laraba a Abuja.

Dokta Gafar Alawode, babban jami’in gudanarwa na DGI Consult, ya jaddada bukatar yin garambawul a fannin samar da kudaden kiwon lafiya domin magance nakasu da aka dade ana yi a fannin kula da lafiyar mata da kananan yara a fadin kasar nan.

Ya jaddada bukatar kananan gwamnatocin kasashe su rungumi dabarun da ake amfani da su wajen samar da bayanai tare da fassara alkawurran kudi zuwa sakamako masu iya aunawa.

Ya ce “manufofin bitar sun hada da yada muhimman abubuwan da aka gano daga nazarin kashe kudaden kiwon lafiyar jama’a da bayar da shawarar kara zuba jari a wuraren da suka fi fifiko.

“Har ila yau, muna neman raba shawarwarin manufofi da kuma tabbatar da aniyar masu ruwa da tsaki don inganta rabon albarkatun kasa.

“Masu ruwa da tsaki za su tsara hanyoyin da za su bi don aiwatar da shawarwarin manufofin da kuma gano dabarun inganta kudaden kiwon lafiyar jama’a, musamman ma a matakin farko na kiwon lafiya (PHC) da Maternal Neonatal and Child Health (MNCH) a matakin jihohi da kananan hukumomi.”

Dokta Bukola Shittu-Muideen na DGI Consult ta gabatar da sakamakon binciken da aka yi na kashe kudade na baya-bayan nan, inda ta gano matsalolin da ke tattare da tsarin tare da ba da shawarar inganta aiwatar da kasafin kudi.

Ta bukaci gwamnatocin jihohi su yi amfani da hanyoyin da suka dogara da shaida don tsara albarkatu da tsara dabarun kiwon lafiya.

Masanin kiwon lafiya na UNICEF, Dokta Sachin Bhokare, ya yaba da kokarin hadin gwiwa na masu ruwa da tsaki a taron, yana mai cewa “wannan shi ne batun daidaita abubuwan da muka sa a gaba don tabbatar da cewa babu mace ko yaro da aka bari a baya.

“Har ila yau, game da haɗa hannun jari mai dorewa zuwa ingantaccen sakamako na kiwon lafiya da rage yawan mace-macen mata da yara.”

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa ma’aikatun lafiya na jihohi, hukumomin bunkasa kiwon lafiya a matakin farko na jiha da ma’aikatun kananan hukumomi sun ba da gudunmawa wajen tattaunawa, lamarin da ke nuna damuwar da ake da ita game da ci gaba da samun gibin kudade a fannin kiwon lafiya.

Wakilan sun amince da kalubalen rashin aiwatar da kasafin kudi tare da jaddada shirye-shiryen yin garambawul, musamman a matakin kananan hukumomi inda aikin ya fi muhimmanci. (NAN) (www.nannews.ng)

FOF/HA
=======
Hadiza Mohammed-Aliyu ta gyara


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *