Shugaban Kasar Nijar yayi kira ga ‘Yan jaridu da su himmatu don cigaban Afrika

Shugaban Kasar Nijar yayi kira ga ‘Yan jaridu da su himmatu don cigaban Afrika

Spread the love

Shugaban Nijar yayi kira ga ‘Yan jaridu da su himmatu don cigaban Afrika

Kungiya

Daga Muhammad Nasir

Niamey (Kasar Nijar) Agusta, 26, 2024 (NAN) An kalubalanci ‘Yan jaridu masu amfani da harshen Hausa da su himmatu wajen hana yaduwar labarin bogi, dabbaka dajarajar da ci gaban Afrika.

Shugaban Kasar Niger, Brig.-Gen. Abdourahmane Tchiani, ya yi kiran ne a lokacin taron tattaunawa na kwana uku da kaddamar da qungiyar ‘yanjarida masu amfani da harshen Hausa a babban birnin Yamai.

Tchiani ya ce ‘yanjaridu sune idanun al’umma da kuma masu shiga tsakanin mahukunta jagororin gwamnati da al’ummar da a ke mulka.

Shugaban kasar wanda Friministan kasar, Ali Lamine-Zeine, ya wakilta ya jinjinawa ‘yanjaridu na Afrika wajen ayyukansu kuma ya qara kira garesu da su himmatu wajen daukaka darajar kasashen su da Afrika gabadaya.

Bako da mussamman a wajen taron, Manjo Hamza Al’Mustafa murabus, kuma tsohon dogarin Shugaban mulkin Soja na Nijeriya, Marigayi Janar Sani Abacha, ya yabawa kasar Nijar wajen kammala taron.

Al’Mustafa ya yi kira ga ‘Yanjaridu su himmatu wajen karfafa kasashen su ta hanyoyi daban da suka hada da tattalin arziki, ilmi, lafiya da zaman lafiya don ci gana kasashen.

” Muna kira ga kasashen mu na Afrika mu himmatu wajen zakulo ma’adananmu, noma da kiyo da sauran harkokin tattalin arziki don ci gaban mu, ” Al’Mustafa ya yi kira

Da take magana bayan kaddamar da kungiyar, shugaba ta farko, Hajiya Mariama Sarkin-Abzin, ta yaba kazon himmar ‘yanjaridun masu aiki da harshen Hausa Kuma ta yi kira da su kara jajircewa a ayyukansu.

Sarkin-Abzin ta ki kira ga ‘Yanjaridu su kara himmatuwa wajen samun ‘yancin ‘aikin ‘yanjarida, walwala da fadin albarkatun baki.

Kamfanin Dillancin Labarin Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa mahalarta taron sun fito daga kasashen; Nijeriya, Nijar, Chadi, Mali, Burkina Faso, Sudan, Benin, Togo, Ghana, Kamaru da Côte d’Ivoire. (NAN) (www.nannews.ng)

BMN/

======

Tace wa: Bashir Rabe Mani


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *