Mutane 7 sun bace, gidaje sun lalace sanadiyyar ambaliyar ruwa a jihar Neja

Mutane 7 sun bace, gidaje sun lalace sanadiyyar ambaliyar ruwa a jihar Neja

Spread the love

Mutane 7 sun bace, gidaje sun lalace sanadiyyar ambaliyar ruwa a jihar Neja

Ambaliyar ruwa
Daga Rita Iliya
Minna, 30 ga Agusta, 2024 (NAN) Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA) ta ce akalla mutane bakwai ne suka bace a kananan hukumomin Magma da Mashegu, biyo bayan wata ambaliyar ruwa da ta afku a ranar Juma’a.

Babban Daraktan Hukumar, Alhaji Abdullahi Baba-Arah, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Minna.

Baba-Arah ya ce sama da gidaje 89 da daruruwan filayen noma ne bala’in ya lalata.

Ya kuma ce, ambaliyar ruwan ta yi awon gaba da motoci uku, wanda ya biyo bayan mamakon ruwan sama da a ka yi da sanyin safiya wanda a ka shafe sa’o’i da dama.

Ya ce: “NSEMA ta samu rahoton ambaliyar ruwa a yankin Mashegu da karamar hukumar Magama.

“ Ambaliyar ruwan ta faru ne sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da a ka tafka tun da sanyin safiyar Juma’a, tun daga karfe biyu na safe zuwa tsakar rana.

“Ya zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, an bayyana bacewar mutane bakwai, sama da gidaje 89 ne lamarin ya shafa, daruruwan kadada na gonaki da motoci uku sun tafi.”

Baba-Arah ya ce yankunan da lamarin ya shafa sun hada da Sabon Pegi da kewaye a Mashegu da Nassarawa a cikin garin Magama.

Ya ce ana ci gaba da aikin ceto da ma’aikatan hukumar tare da ‘yan sa kai domin ceto mutanen da suka bata. (NAN)(wwwnannews.ng)

RIS/USO/HMH
Sam Oditah ya gyara

 


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *