Hatsarin jirgin ruwa a Sokoto ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 41, an ceto mutane 11 – NIWA

Hatsarin jirgin ruwa a Sokoto ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 41, an ceto mutane 11 – NIWA

Spread the love

Hatsarin jirgin ruwa a Sokoto ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 41, an ceto mutane 11 – NIWA

Mishap

Daga Habibu Harisu

Sokoto, Agusta 21, 2026 (NAN) Hukumar Kula da Hanyoyin Ruwa ta Cikin Gida ta Kasa (NIWA) ta tabbatar da cewa mutane 41 sun mutu sannan aka ceto wasu 11 a wani hatsarin kwale-kwale a yankin Gorau da ke kan Kogin Goronyo a karamar hukumar Goronyo ta jihar Sokoto.

Manajan Yankin NIWA da ke Sokoto, Mista Abdulkadir Yusuf, ya sanar da hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ranar Alhamis a Sokoto.

Yusuf ya ce jirgin ruwan yana dauke da kimanin mutane 82, ciki har da shugaban al’umma da ke kan hanyarsu ta zuwa gonar shinkafa don girbi.

Ya ce an binne gawarwakin a cikin al’ummomi daban-daban, yayin da 11 da suka tsira suka sake haɗuwa da iyalansu, ya ƙara da cewa ana ci gaba da neman mutanen da suka ɓace.

Yusuf, wanda ya ce lamarin ya faru ne a ranar Laraba, ya danganta hakan da sakaci, yawan mutanen cikin kwale-kwale da kuma karya dokokin tsaro.

Ya bayyana cewa wata tawaga da ta kunshi jami’ai daga NIWA, Hukumar Kula da Gaggawa ta Kasa (NEMA), Hukumar Kula da Gaggawa ta Jiha (SEMA), Kungiyar Red Cross da kuma masu aikin sa kai na yankin suna wurin.

Manajan Yankin ya sake nanata cewa NIWA ta daɗe tana jan hankalin al’ummomin da ke bakin kogin kan matakan tsaro, jagorori, amfani da rigunan ceto da sauran abubuwan da suka shafi amfani da ruwa.

Kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito cewa ana samu rahotannin faruwar abubuwa da dama a gefen kogin Sokoto-Rima kusan kowace shekara a jihar Sokoto.(NAN)(www.nannews.ng)
HMH/ YMU
An gyara ta Yakubu Uba
=======


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *