Gwamnonin Jihohin Najeriya sun jaddada kudirinsu ga cigaban yara kanana

Gwamnonin Jihohin Najeriya sun jaddada kudirinsu ga cigaban yara kanana

Spread the love

Daga Emmanuel Oloniruha

Abuja, Agusta 14, 2026 (NAN) Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ta sake jaddada alƙawarin da dukkan gwamnonin jihohi 36 suka ɗauka na sanya tallafawa cigaban yara kanana (ECD), a matsayin muhimmin abu a cikin ajandar cigaban ɗan adam ta Najeriya.

An sake jaddada wannan alƙawarin ne tare da haɗin gwiwar Bankin Duniya, cigaban dan adam (HCD) da ma’aikatar kasafin Kuɗi da tsarin Tattalin Arziki.

Daraktan yada labarai da sadarwa na NGF, Yunusa Abdullahi, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja, cewa babban darakta na Sakatariyar NGF, Dr Abdulateef Shittu, ya yi alƙawarin a wani taron ba da shawara kan harkokin kuɗi na yankin Arewa maso Yamma kan ECD.

Shittu, wanda Abdullahi ya wakilta a taron bitar, ya bayyana jarin da aka zuba a farkon shekarun, a matsayin jarin da aka zuba na dogon lokaci a fannin lafiya, ilimi, tsarin aiki da kuma makomar tattalin arziki a Najeriya.

“Lokacin da yaro ke ciki har zuwa shekaru biyar na farko na rayuwa, yana wakiltar wani muhimmin kafar ci gabansa.”

“A cikin waɗannan shekarun ne aka kafa harsashin lafiya, ilmantarwa, cigaban fahimta da kuma samar da aiki a nan gaba,” in ji shi.

Daraktan ya bayyana cewa, dole ne Najeriya ta dauki ECD a matsayin muhimmin ci gaba da tattalin arziki, maimakon a matsayin wani shiri da ya takaita ga wani fanni guda.

“Saboda haka, saka hannun jari a ci gaban yara tun suna ƙanana, ba wai kawai jari ne ga yara ba, har ma da saka hannun jari a al’ummar Najeriya da kuma ci gaban tattalin arziki na dogon lokaci,” in ji Shittu.

Ya jaddada cewa, za a tantance ingancin manufofin ECD na ƙasa, ta hanyar fassara su zuwa shirye-shirye na zahiri a matakin ƙasa da ƙasa.

“Duk da cewa manufofi da tsare-tsare na ƙasa suna ba da muhimmin alkibla, tasirinsu a ƙarshe zai dogara ne akan yadda aka mayar da su aiki yadda ya kamata, a matakan jiha da ƙananan hukumomi.

“Wannan ya sanya mu, masu ruwa da tsaki a harkokin gwamnati, a tsakiyar ajandar ECD ta Najeriya,” in ji shi.

Bugu da kari, Shittu ya lura cewa sarkakiyar ECD tana buƙatar tsarin haɗin gwiwa da daban-daban da zai shafi dukkan fannoni masu dacewa, domin babu wata ma’aikata guda ɗaya da za ta iya samar da nau’ikan ayyukan da yaro ke buƙata don bunƙasa.

“Dole ne dukkan sassan su yi aiki tare don cimma sakamako iri ɗaya ga yara,” in ji shi.

Shittu ya ƙara yin gargaɗi game da ɗaukar tsarin da muhimmanci, a matsayin wani abu da zai kawo cigaba, yana mai jaddada muhimmancin aiwatarwa, kuɗaɗen da za a kashe, daidaitawa da kuma ɗaukar alhakin da ya dace.

“Tsammaninmu shi ne cewa, wannan tsari ya wuce tsarin tsara shirye-shirye.”

Ya ƙara da cewa, “Shirye-shiryen da aka tsara a nan, ya kamata su samar da hanya bayyananna don aiwatarwa, daidaitawa, kuɗi da kuma riƙon amana, kuma mafi mahimmanci, ya kamata a haɗa su cikin tsare-tsaren jiha da kasafin kuɗi da ake da su a yanzu.”

Hakazalika, ya yi alƙawarin cewa Sakatariyar NGF, za ta ci gaba da amfani da hadin gwuiwa da ilmantarwa tsakanin takwarorinta, don tallafawa jihohi wajen ƙarfafa tsarin ECD ɗinsu.

A karshe Daraktan, ya yi kira ga mahalarta taron da su yi amfani da wannan damar wajen samar da tsare-tsare masu inganci wadanda za su iya samar da ingantattun sakamako ga kananan yara. (NAN)(www.nannees.ng)

 

OBE/AAA/FOF

Fassarar Aisha Ahmed


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *