Tinubu ya taya al’ummar musulmi murnar Mauludi

Tinubu ya taya al’ummar musulmi murnar Mauludi

Taya murna

By Salif Atojoko

Abuja, Satumba 15, 2024 (NAN) Shugaban kasa Bola Tinubu ya taya al’ummar Musulmin Najeriya murnar zagayowar Mauludin Annabi Muhammadu na wannan shekara. 

Tinubu ya bukaci al’ummar Musulmi da su yi amfani da wannan lokacin wajen zurfafa tunani da tunawa da kyawawan halaye da koyarwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama.

Mista Bayo Onanuga, mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai da dabaru ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja.

“Yayin da muke bikin Mauludi, ya kamata mu yi tunani a kan irin rayuwar da Annabi Muhammad ya yi, wanda ya nuna tsafta, rashin son kai, juriya, kyautatawa da tausayi. Dole ne mu yi ƙoƙari mu kwatanta waɗannan kyawawan halaye, ”in ji shi.

Shugaba Tinubu ya kuma bukaci al’ummar Musulmi da su sadaukar da ranar Mauludi domin yi wa kasa addu’a da kuma tausayawa juna.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Mista Olubunmi Tunji-Ojo, ministan harkokin cikin gida, a ranar Juma’a, ya ayyana ranar Litinin a matsayin ranar hutu domin bikin Mauludin na bana.(NAN) (www.nannews.ng).

SA/IS

====

Edited by Ismail Abdulaziz

Ambaliyar ruwa a Maiduguri: Hukumar gidajen yari ta ce fursunoni 281 sun bace

Ambaliyar ruwa a Maiduguri: Hukumar gidajen yari ta ce fursunoni 281 sun bace

 

Fursunonin
Daga Ibironke Ariyo
Abuja, Satumba 15, 2024(NAN) Hukumar da ke kula da gidajen yari ta Najeriya NCoS ta bayyana cewa fursunoni 281 sun bace bayan kwashe fursunonin da jami’an hukumar tare da goyon bayan sauran jami’an tsaro suka yi zuwa wani wuri daban.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar (SPRO), Mista Abubakar Umar, ya fitar ranar Lahadi a Abuja.

Hukumar ta NCoS ta kuma ce an sake kama wasu fursunoni bakwai.

Umar ya ce hukumar na da bayanan fursunonin da suka bace, ciki har da na’urar tantancewa.

“Ambaliyar ta rusa katangar wurare daban da am na gidan, ciki har da matsakaitan gurin tsaro na Maiduguri (MSCC) wanda ma’aikatan da ke cikin birnin.

“Bayan kwashe fursunonin da jami’an ma’aikatar tare da goyon bayan jami’an tsaro suka yi zuwa wani wuri mai tsaro, an ga fursunoni 281 sun bace.

“Duk da haka, yana da mahimmanci a lura cewa ma’aikatan suna tsare da bayanansu, gami da na’urar tantancewa, wanda ake bai wa jama’a.

“ Hukumar na aiki tare da sauran hukumomin tsaro saboda an fara aiki a ɓoye da kuma a bayyane don gano su.

“Yanzu haka, jimlar fursunoni bakwai (7) an sake kama su, kuma an mayar da su gidan yari, yayin da ake kokarin zakulo sauran da kuma dawo da su a tsare.

“Yayin da ake ci gaba da wannan kokarin, jama’a na da tabbacin cewa lamarin ba zai kawo cikas ba ko kuma ya shafi lafiyar jama’a.” (NAN) (www.nannews.ng)

ICA/SH

=====
Sadiya Hamza ta gyara

Shettima ya jagoranci gangamin karshe na jam’iyyar APC na zaben gwamnan Edo

Shettima ya jagoranci gangamin karshe na jam’iyyar APC na zaben gwamnan Edo

Rally

Usman Aliyu

Benin, Satumba 14, 2024 (NAN) Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima a ranar Asabar ya jagoranci tawagar jiga-jigan jam’iyyar APC zuwa Benin, babban birnin jihar Edo, domin gangamin karshe gabanin zaben gwamnan da za a yi ranar 21 ga watan Satumba.

Daga cikin jiga-jigan jam’iyyar APC da suka halarci taron akwai shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, shugaban jam’iyyar na kasa Abdullahi Ganduje, gwamnonin jihohi da sauran su.

A nasa jawabin, Shettima ya bayyana dan takarar jam’iyyar APC, Monday Okpebolo, a matsayin gogaggen shugaban da ya kware a tarihi.

A cewarsa, Okpebolo shine mutumin da ya dace ya kai Edo mataki na gaba.

Ya jaddada muhimmancin hadin kai da zaman lafiya wajen samun ci gaba, inda ya bayyana cewa ” sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ba tare da bata lokaci ba yana nuna himma wajen fifita muradun Edo a kan komai”.

A cewarsa, tare da karin kudaden da ake rabawa jihohi, kamata ya yi gwamnati mai zuwa ta samu isassun kayan aiki don bankado ayyukan raya kasa.

A nasa jawabin, Ganduje ya bukaci masu zabe da su kada kuri’a ga dan takarar jam’iyyar APC.

“ Kasa tana da albarka domin burin jam’iyyarmu ya bunkasa. Edo ya zama alama ce ta farfadowar tattalin arziki,” inji shi.

Shugaban jam’iyyar APC na kasa ya yabawa shugabancin jam’iyyar na jihar, inda ya jaddada cewa jajircewarta ba ta gushe ba.

Da yake jawabi jim kadan bayan ya karbi tutar jam’iyyar APC, Okpebolo ya yi alkawarin farfado da tattalin arzikin jihar.

Dan takarar jam’iyyar APC ya ce jihar  Edo ta dade tana shan wahala, inda ya ce zaben fitar da gwani na PDP shi ne kadai hanyar dawo da fata.

“Mun zabi harkar ilimi, tsaro, da ababen more rayuwa, da kiwon lafiya da noma.

“Ga bangaren noma, za mu samar da rance ga manoma da rance mai sauki ga matan kasuwar mu,” inji shi.

Dan takarar na jam’iyyar APC ya yi alkawarin daukar malamai 10,000 aiki, inda rabin wannan adadi ya zo cikin kwanaki 100 na farko.

Ya yi alkawarin kafa dokar ta-baci kan ababen more rayuwa, inda ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda tituna ke cikin jihar.

Sauran jiga-jigan da suka yi jawabai sun sun hada da Akpabio da Sanata Adams Oshiomhole da kuma Gwamna Bassey Ottu na Kuros Riba. (NAN) (www.nannews.ng)

AUO/ETS

======

Shugaban kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya bukaci likitoci su cigaba da jajircewa

Shugaban kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya bukaci likitoci su cigaba da jajircewa

Likitoci

Daga Habibu Harisu

Sokoto, Satumba 14, 2024 (NAN) Manajan Daraktan Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), Malam Ali M. Ali, ya bukaci likitoci da su ci gaba da jajircewa, mayar da hankali, da sadaukar da kai wajen yi wa bil’adama hidima.

Ali ya ba da wannan nasihar ne a ranar Asabar a Sakkwato a wajen bikin yaye daliban jami’ar Sudan International University (SIU) da kuma daliban Kwalejin Kiwon Lafiyar Hayat da suka karasa karstu a Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sakkwato (UDUS) na shekarar 2023.

Ya kuma bukaci daliban da a ka yaye da su rike kyawawan dabi’u, kuma su rika nuna kwazo, mutunci, mutuntawa da tarbiyyar da aka cusa musu a lokacin karatunsu.

Ali ya bukace su da su dauki gwagwarmayarsu ta ilimi da muhimmanci domin tana cike da kalubale duba da irin rikicin da ya barke a Sudan a tsakiyar karatunsu.

”A matsayina na mahaifin ɗaya daga cikin waɗanda suka kammala karatun, ina jin daɗi, alfahari da gamsuwa ganin da tafiyar da aka fara da nisa ta zo ƙarshe.

”Buri ne ya cika ga ɗana, yayin da na so ya karanta Kimiyyar Kwamfuta amma ya nace ya zama Likita.

“Na tuna cewa mahaifina yana son in karanta aikin likita, amma na nace Sai  karanta aikin jarida, don haka mafarkin mahaifina ya bayyana a rayuwar jikansa, na gamsu,” in ji Ali.

Ya ce daliban da suka kammala karatun sun fuskanci kalubale domin a shekararsu ta farko da suka yi karatu, an hambarar da gwamnatin Shugaba Umar Al-Bashir, da. COVID-19 da rikicin shugabanci a Sudan.

Ya bayyana cewa, wani kalubalen da suka fuskanta shi ne kudin da suka fara a lokacin da Dalar Amurka ta kai kusan Naira 250 kuma kafin su kammala karatunsu ya kai kusan N1,300 ko sama da haka.

“Kada ku bar wani shine da zai hana ku neman nasara don ba ta zuwa da sauƙi. Kada ka bari abubuwa da yawa su datse mafarkinku da burinku.

“Ku yi amfani da ilimin da ku ka samu daga malamanku, ku fuskanci nayuwa mai kyau, don kun zama taurari masu haske kuma ku kasance masu dagewa da hidima ga ‘yanuwaku’ yan adam.

“Ba shakka cewa darussan da kuka koya a cikin karatun da kuma daga iyayenku, za su ci gaba da jagorantar ku ta hanyar rayuwa,” in ji Ali.

Wani mahaifin, Haruna Adiya, ya bayyana cewa taron ya kasance abin tunawa don ganin irin jarin da suka dukufa da kuma sadaukarwar da daliban suka yi.

A jawabinsa na bajinta, wani dalibi da ya kammala digiri, Muhammad Ali, dan shugaban NAN, ya bayyana tafiyar a matsayin kalubale.

”Wannan yana nuni da cewa muna da damar samun karin nasarori. Don zama Likitoci kwararru Kuma wanna nasarar wani kira ne don yi wa bil’adama hidima.”

Wata wacce ta kammala digiri, Sakina Mu’azu, ta yaba da sadaukarwar da Farfesoshi da sauran malamai suka yi duk da dimbin kalubalen da suka fuskanta kamar yakin Sudan a lokacin karatunsu.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa akalla mutane 64 ne a ka yaye a fannonin likitanci, Pharmacy, Biomedical Engineering, Clinical Sciences da sauran kwasa-kwasai da sauransu. (NAN)(www.nannews.com)

HMH/BRM

Bashir Rabe Mani ne ya tace

Sojoji sun ceto mutane 13 da aka yi garkuwa da su, sun kwato makamai da alburusai a Kaduna

Sojoji sun ceto mutane 13 da aka yi garkuwa da su, sun kwato makamai da alburusai a Kaduna

Daga Tijjani Mohammad

Sojoji

Kaduna, Sept.14, 2024 (NAN) Dakarun Sector 4 Operation Whirl Punch sun kubutar da wasu mutane 13 da aka yi garkuwa da su a wani wurin masu garkuwa da mutane a karamar hukumar Kachia ta jihar Kaduna.

Kwamishinan tsaron gida da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Kaduna.

Aruwan ya ce “bisa bayanin da rundunar ta samu ga gwamnatin jihar Kaduna, sojojin sun mayar da martani ga sahihan bayanan sirri na ‘yan bindigar da suka yi garkuwa da wadanda aka sace a kauyen Chigulu, karamar hukumar Kachia.”

Ya ce daga baya ne sojojin suka yi hattara domin gudanar da aikin ceto a wurin da ake zargin ‘yan bindigar na da sansani.

Ya kara da cewa “dakarun sun isa wurin inda suka tunkari ‘yan fashin.

“An yi wani kazamin fada da musayar harbin bindigu a gindin wani tsauni da ke yankin.

“An fatattaki ‘yan bindigar sun gudu zuwa cikin daji, suka kuma yi watsi da wadanda suka yi garkuwa da su.

“Jami’an tsaro sun ceto mutanen 13 da aka yi garkuwa da su, wadanda suka hada da maza shida da mata bakwai daga maboyar.”

A cewarsa, sojojin sun tarwatsa sansanin, tare da lalata kayayyaki daban-daban, kamar su tufafi da abubuwan da suka shafi kayan fada a wurin.

Ya ce “an kwato wasu kayayyaki da suka hada da bindiga AK-47 guda daya, bindugu ma su linzami guda hudu, alburusai 87 7.62mm, kananan na’urorin hasken rana guda biyar, wayoyin hannu biyar da tsabar kudi N192,220.”

Aruwan ya bayyana cewa an kai wadanda aka ceto zuwa wani sansanin soji domin duba lafiyar su, kafin a sada su da iyalansu.

Ya ce Gwamna Uba Sani ya bayyana farin cikin sa da rahoton, ya yaba da yadda rundunar ta mayar da martani cikin gaggawa, karkashin jagorancin babban kwamandan runduna ta daya ta sojojin Najeriya/Commander Operation Whir, l Punch (OPWP), Manjo Janar Mayirenso Saraso, kuma ya taya su murnar nasarar aikin.

Ya ce gwamnan ya mika sakon fatan alheri ga wadanda aka ceto yayin da suka fatan su koma cikin iyalansu lafiya. (NAN)(www.nannews.ng)

TJ/BRM

Bashir Rabe Mani ne ya tace

Iyaye sun jaddada mahimmancin koyar da harsunan asali

Iyaye sun jaddada mahimmancin koyar da yara harsunan asali

Harshe

By Veronica Dariya/ Uche Bibilari

Abuja, Satumba 14, 2024 (NAN) Wasu iyaye a babban birnin Tarayya Abuja sun jaddada mahimmancin koyar da yara harsunan asali don ci gaban rayuwarsu.

A wata tattaunawa ta musamman da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya yi a ranar Asabar, iyaye sun nuna gazawa wajen koyar da harsunansu na asali ga yaran da suka haifa amma sun bayyana aniyarsu na farfado da yin hakan.

Sun yi nuni da cewa, a hankali harsuna da al’adu da dama suna bacewa, kuma akwai bukatar a maido da al’adu cikin hanzari.

Mista Femi Ogunshola, wani ma’aikacin gwamnati, ya ce yin magana da yarukan asali ga yara ya taimaka wajen kiyaye al’adu da fahimtar salon rayuwarsu.

Ya yarda da kasa koyar da ‘ya’yansa Yarabanci amma tun a lokacin da ya yi kokarin yin magana da su sai ya fahimci matsalar. 

“A gare ni, ina jin Yarbanci da Ingilishi, ga ’ya’yana; Abin baƙin ciki, sun fahimci harshen amma da wuya su iya magana da shi.

“Ina ganin kaina a matsayin gazawa a wannan bangaren. Magana da yarenku na asali yana taimakawa wajen kiyayewa da fahimtar al’adu domin harshe wani bangare ne na al’ada.

“Da zarar kun fahimci harshenku, babu shakka za ku fahimci al’adun, wanda shine hanyar rayuwa,” in ji shi.

Misis Chioma Okpara, wata ma’aikaciyar gwamnati, ta ce wasu ‘yan Najeriya na barin yarensu da al’adunsu, inda suka rungumi al’adun kasashen waje maimakon haka.

Ta kuma jaddada muhimmancin yin magana da yarukan gida ga yara, ko da a bainar jama’a, ta kuma nuna damuwa kan yadda iyaye ke jin kunyar yin hakan.

“A matsayina na ’yar kabilar Ibo da ta auri Bayerabe, a kullum ina jin yarena da ‘ya’yana saboda haka aka rene ni.

“Ko da yake sun fahimci yaren sosai, har yanzu suna fuskantar wahalar yin magana da kyau – har yanzu aiki ne a gaba a koyar dasu tun suna kanana.

“Na yi imani cewa da lokaci, za su yi magana da kyau sosai. Ba na yin turanci da yarana, ko muna gida ko a waje.

“Ba Igbo kawai nake magana ba amma yare na da su. Ba na jin kunyar magana da yarena a duk inda na samu kaina,” in ji ta.

Har ila yau, Dokta Olufunke Onaadepo, babban malami, ya yi gargadin cewa lokutta masu zuwa za su iya yin gwagwarmayar sadarwa a cikin harsunansu na asali saboda iyaye suna ba da fifiko ga harsunan Yammacin Turai.

“Al’ummai masu zuwa da muke reno ba za su iya yin magana a cikin harsunanmu na asali.

“Wannan ya faru ne saboda yawancin iyaye, musamman manyan mutane, suna renon yara da amfani da harsunan Yamma.

” Da yawa daga cikinmu suna tunanin muna nuna kwarewa ta yin hakan. Abin takaici, a hankali muna rasa al’adunmu. Da kaina, na fahimci hakan a makare,” in ji ta.

Sauran iyaye da suka hada da Mrs Ruth Hassan da Mrs Rabi Suleiman, sun bayyana abubuwan da suka faru tare da jaddada muhimmancin koyar da yarukan asali ga yara.(NAN) ( www.nannews.ng )

DVK/UU/DE/AMM

==============

Dorcas Jonah da Abiemwense Moru ne suka gyara

Ambaliyar Ruwan Maiduguri: Hukumar NEMA, Sojoji, da sauransu sun kara kaimi wajen ceto, yayin da mutane da dama suka makale

Ambaliyar Ruwan Maiduguri: Hukumar NEMA, Sojoji, da sauransu sun kara kaimi wajen ceto, yayin da mutane da dama suka makale

Ceto

By Yakubu Uba 

Maiduguri, Satumba 12, 2024 (NAN) Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) da sojoji da sauran kungiyoyi sun kara kaimi wajen ceto jama’a da dama da suka makale ko kuma suka bace, kwanaki biyu bayan ambaliyar ruwa a Maiduguri.

Mukaddashin Shugaban Hukumar NEMA na shiyyar Arewa maso Gabas, Sirajo Garba ne ya bayyana haka a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Maiduguri ranar Alhamis.

Ya ce an ceto wasu mutane da dama da suka makale a gidajensu a ranar Alhamis.

“Mun baza, manyan motoci da jiragen ruwa kuma sojoji suna aikin bincike da ceto mutane musamman a unguwannin Abbaganaram, Muna, da kuma gidaje 505.

“A bangaren mu a matsayin NEMA, mun ceto mutane kusan 200 tsakanin jiya da yau.

“A ranar da lamarin ya faru, an ceto sama da mutane 1,000, yayin da sama da 70,000 sun bayyana a sansanoni bakwai.”

Dangane da adadin wadanda suka mutu, Garba ya ce: “Ba za a iya tantance adadin ba a yanzu”, ya kara da cewa kawo yanzu NEMA ta bayar da jakunkuna guda hudu.

“Yayin da ruwa ke ci gaba da ja da baya, za mu iya samun wasu gawarwakin,” in ji Garba.

A halin da ake ciki, mambobin kungiyar gwamnonin Najeriya karkashin jagorancin shugabanta kuma gwamnan jihar Kwara, Alhaji Abdultahman Abdulrazak, sun isa Maiduguri domin jajantawa gwamnati da jama’ar jihar.

Sauran wadanda suka kai ziyarar sun hada da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Ganduje, da ministocin albarkatun ruwa, cikin gida, noma, da wasu ‘yan majalisar dokokin kasar. 

NAN ta ruwaito cewa Gwamna Ahmadu Fintiri a yayin ziyarar ya bayar da gudunmawar Naira miliyan 50, yayin da dan majalisar wakilai Muktar Betara (APC-Borno) ya bayar da Naira miliyan 100. (NAN)

YMU/ SH

=======
Sadiya Hamza ta gyara

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham

Shugaba Bola Tinubu ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham da ke birnin Landan na kasar Birtaniya ranar Laraba

Ganawa

By Salif Atojoko

Abuja, Satumba 12, 2024 (NAN) A ranar Laraba ne Sarki Charles III ya tarbi shugaban kasar Najeriya, Bola Tinubu, a fadar Buckingham da ke birnin Landan na kasar Birtaniya domin wata ganawar ta musamman.

Mista Bayo Onanuga, mai baiwa shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai da dabarun sadarwa, ya fada a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, ya ce taron ya nuna kyakykyawan alakar da ke tsakanin Najeriya da Birtaniya.  

Ya ce wannan shi ne ganawar shugabannin biyu na farko tun bayan da suka hadu a Dubai a taron COP 28 na yanayi a bara. 

“Taron na baya-bayan nan ya kasance bisa bukatar Sarki.

“Dukkan shugabannin biyu sun tattauna batutuwan da suka shafi zamantakewar duniya da na shiyya-shiyya, inda suka mai da hankali kan kalubalen gaggawa da sarkakiya na sauyin yanayi,” in ji Onanuga.

Ya ce Tinubu da Sarki Charles sun kuma binciko yiwuwar yin hadin gwiwa tare da sa ran taron COP 29 da za a yi a Azerbaijan da kuma taron shugabannin kasashen Commonwealth (CHOGM) a Samoa.

“Shugaba Tinubu ya nanata kudurin Najeriya na ganin an magance sauyin yanayi ta hanyar da ta dace da manufofin tsaron makamashin kasar yayin da ya tabbatar da a shirye Najeriya take ta rungumi dabarun zamani na duniya don dorewa. 

Onanuga ya ce “A yayin tattaunawar tasu, shugabannin biyu sun yi musayar ra’ayoyi kan sabbin hanyoyin samar da kudade, tare da bayyana sha’awar juna wajen karfafa hadin gwiwa ta hanyar amfani da matsayin shugabancin Najeriya a Afirka da kuma Commonwealth,” in ji Onanuga. (NAN) (www.nannews.ng)

SA/AMM 

=====

Abiemwense Moru ne ya gyara

Wadatar abinci ita ce fifikon Gwamnatin Tarayya – Minista

Wadatar abinci ita ce fifikon Gwamnatin Tarayya – Minista

Abinci

By David Adeoye

Iseyin (Jihar Oyo) Satumba 11, 2024 (NAN) Ministan Albarkatun Ruwa da Tsaftar muhalli, Mista Joseph Utsev, ya ce wadatar abinci a Najeriya shi ne abin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta sa gaba.

Utsev ya bayyana haka ne a ranar Larabar da ta gabata a yayin wani rangadin tantancewa a sashen kula da noman rani na ” Centre Pivot Irrigation Project” da ke Iseyin a jihar Oyo.

A cewar ministan, aikin samar da abinci, samar da ayyukan yi da inganta tattalin arzikin kasa ya yi daidai da ajandar manufofin shugaban kasa.

Ya kuma jaddada kudirin gwamnatin tarayya na samar da kayayyakin da ake bukata wadanda za su bunkasa samar da abinci.

Ya ce ci gaba da bai wa sashen noman rani na jihar Ogun hadin gwiwa da cibiyar samar da wutar lantarki ta kasa, wani bangare ne na kokarin karfafa noman rani.

“An fara aikin noman rani na Middle Ogun a shekarar 1990, kuma manufar aikin shine a samar da fili kimanin hekta 12,000 a noman.

“Lokacin da aka fara aikin an yi amfani da man dizal ne wajen samar da wutar lantarki amma yanzu mun canza tsarin samar da wutar lantarkin zuwa hasken rana da wutar lantarki ta kasa saboda tsadar mai na dizal da wasu dalilai,” inji shi. .

Ministan ya bayyana cewa an kai kashi 95 cikin 100 na aikin hada cibiyar da cibiyar sadarwa ta kasa, yayin da aikin bayar da agajin gaggawa ya kai matakin kamala na kashi 85 cikin 100.

“Daga abin da muka gani a yanzu, za mu iya cewa tsarin da ke gudana zai iya kai ga kammalluwar ayyukan.

“ Kuma, za a fara gyaran dukkan sauran wuraren ban ruwa nan ba da jimawa ba, kuma cibiyar za ta fara aiki gadan-gadan nan da shekaru biyu zuwa uku masu zuwa.

“Don haka, za a fara aiki da dukkan fadin hecta 12,000 na fili da muka yi niyyar samarwa,” in ji shi.

Alhaji Dauda Ademola, shugaban kungiyar manoman aikin noman rani ta Ogun ta tsakiya, Iseyin, ya yabawa gwamnatin Tarayya bisa gaayyukan da take gudanarwa a cibiyar.

Ademola ya bukaci gwamnati da ta kara himma wajen ganin an gaggauta kammala ayyukan da sauran kayayyakin da za su bunkasa noman rani. (NAN) (www.nannews.ng)

DAK/CHOM/MAS

===========

Chioma Ugboma da Moses Solanke ne suka gyara

Wani kamfanin Burtaniya ya ƙaddamar da dandamalin haɓaka harsunan Najeriya, al’adu da kayan tarihi

Wani kamfanin Burtaniya ya ƙaddamar da dandamalin haɓaka harsunan Najeriya, al’adu da kayan tarihi

Al’adu

By Ibukun Emiola

Ibadan, Satumba 11, 2024 (NAN) Wani kamfanin Burtaniya na fasahar zamani mai aiki da na’ura mai kwakwalwa ya ƙaddamar da samfurin karatu na zamani, ‘AE Learning’, don haɓaka harsuna da al’adun Najeriya tare da haɗakar harshen Jamusanci. 

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa kamfanin mai suna Afro-European Business Services Limited da ke Burtaniya, ya bayyana hakan ne a Ibadan ranar Laraba.

Babban Jami’in Kamfanin, Oluseun Durowoju, ya ce AE Learning shi ne taimaka wa dunkulewar al’adu daban-daban ta hanyar koyar da harsunan asali na Najeriya da sauran na Afirka.

A cewarsa, hanyar koyon an yi ta ne ga duk wanda ke son ya fara daga tushe ko kuma ya fahimci harsuna da al’adu daban-daban.

Ya ce koyon zai fadada zuwa sauran harsunan Afirka don saukaka fahimtar harsunan, da alaka da su da kuma saukakawa ga dalibai.

“Ko dai yaran da aka haifa a wajen Najeriya, wadanda ke da alaka da Najeriya, har ma da yaran da ke cikin Najeriya, wannan samfurin namu da malamanmu za su sa ya zama mai sauki da jin daɗi don koyon kowane yaren,” in ji shi.

Durowoju ya ce samfurin zai bude idanun duniya don fahimtar harsuna da al’adun Afirka da kyau, ta yadda za a inganta jituwa da haɗin kai.

Ya ci gaba da cewa fahimtar harsunan zai ba da ma’ana cika zaman tare, ya kawo canji kuma mafi mahimmanci ya sa mutum ya samu yarda da asalinsu na kakanni.

“Koyon AE an yi niyya ne don samar da samari na yanzu har ma da manya su san harsunansu na asali, baya ga yaren kasuwanci na duniya,” in ji shi.

Durowoju, wanda ya jaddada matsayin Babban Jami’in Ƙirƙirar kafar, ya bayyana cewa kamfanin ya kuma yi niyyar kawo manyan harsunan duniya ga masu sauraro a Afirka cikin sauƙi. 

Wannan, in ji shi, zai samar da damammaki ga ‘yan Afirka na gida da waje, don koyo da kuma zama masu mu’amala da fahimtar harsunan waje daban-daban tare da taimakawa cikin saukin fahimtar wasu al’adu.

Babban Manajan Kayayyakin Kamfanin, Oluseyi Sodiya, ya bayyana kyakkyawan fata game da wannan samfurin, yana mai cewa, wani ra’ayi ne da aka tsara na samar da hanyoyin da za a rage matsalolin harshe wajen ciyar da rayuwar bil’adama gaba.

“Zai taimaka wajen inganta zaman lafiya tsakanin kowace kabila ta hanyar fahimtar al’adun juna, haka kuma zai taimaka matuka wajen inganta harkokin kasuwanci, mu’amalar jama’a da kuma alakoki daban-daban,” in ji Sodiya.

Babban manajan samfurin ya sanar da judanya da mutane 100 na farko don yin rajista na watanni biyu da kuma samun ƙarin watanni biyu kyauta.

“Mafi mahimmanci, dandalin yana da sauƙin amfani kuma yana da sauƙin shiga. An shirya kwasa-kwasan nazarin yarurrukan don nazarin kanmu.

“Za ku iya koyo da kan ku da kuma lokacin ku. Darussan gajeru ne, masu dacewa kuma an ƙirƙiresu ta hanyar umarni na gaske, ”in ji shi. (NAN) (www.nannews.ng)

 

IBK/KOLE/MAS
==========

Remi Koleoso da Moses Solanke ne suka gyara