Annoba a Neja: Matar Tinubu ta ba da gudummawar N1bn ga wadanda abin ya shafa
Daga Celine-Damilola Oyewole
Ambaliya
Minna, 5 ga Agusta, 2025 (NAN) Matar shugaban kasa, Sen. Oluremi Tinubu ta ba da gudummawar Naira biliyan daya don tallafawa mutanen da annoba ta shafa a fadin jihar Neja.
Tinubu, ta bayar da wannan tallafin ta hanyar aikin da ta kirkiro na Renewed Hope Initiative (RHI) a ranar Talata a Minna, ta ce wadanda za su ci gajiyar su ne wadanda ambaliyar ruwa, gobara, da hatsarin kwale-kwale da wadanda harin ‘yan fashi ya shafa.
Ta bayyana annoba a matsayin abin dubawa, inda ta ce, hakika wadannan lokuta ne masu wahala, ta kuma yi adduar Allah ya jikan wadanda suka rasu, tare da ba marasa lafiya wadanda suka jikkata Lafiya.
Uwargidan ta kuma amince da sa hannun gwamnatin tarayya cikin gaggawa, wajen raba kudade da kayayyakin agaji ga wadanda abin ya shafa.
Bugu da kari ta yi nuni da cewa, tausayi yana inganta al’umma ya na kuma kara mata jajircewa a lokutan wahala, inda ta kara da cewa, ya kamata mutane su koyi tausayawa juna.
“Na yi farin ciki da cewa Shugaba Bola Tinubu, ya amince da gaggauta a saki kudade da kayayyakin abinci don taimakawa wajen farfado da gine-ginen da ambaliyar ruwa ta lalata.
“Na zo nan ne domin in jajanta wa Gwamna Mohammed Bago, da al’ummar Jihar Neja, kan mumunar ambaliyar ruwa da ta addabi karamar hukumar Mokwa, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.
“Ina kuma yabawa kokarin gwamnan, na tashi tsaye wajen aiki tare da bayar da gudummawar kudade da abinci, domin tallafawa iyalan da suka rasa matsugunansu.
“Don tallafawa kokarin sake gina jihar Neja, majalisar gudanarwar kungiyar Renewed Hope Initiative, ta bayar da gudummawar Naira biliyan daya, tare da kayayyakin agaji.
“Kayayyakin sun hada da tufafi, takalma, da buhunan shinkafa 50,000 ga jihar ta Neja,” inji Uwargidan shugaban kasa Tinubu.
Mai dakin shugaban Kasar ta kuma jajantawa wadanda hatsarin kwale-kwale ya rutsa da su, da wadanda harin ‘yan bindiga ya rutsa da su, kana da wadanda suka ibtila’in gobara a jihar.
“A matsayina na uwa, na yi imanin cewa dukkanmu za mu iya shawo kan wannan bala’i tare da taimakawa al’umma ta wartsake. Allah ya baku lafiya, ya kuma jikan wadanda suka rasu.
“Za a yi amfani da kudaden wajen bada tallafin gidaje da muhimman kayayyaki, don a taimakawa iyalan wadanda suka rasa matsugunansu domin su dawo kan kafafunsu,” Uwargidan ta ce.
Haka kuma, ta jaddada cewa wannan ya yi daidai da manufar shirin nata, kamar yadda yake kunshe a taken su “Ingantacciyar Rayuwa zuwa ga Iyalai”.
Kamfanin Dillancin labarai na kasa (NAN), ya ruwaito cewa, gwamnan Neja, Umar Bago, ya yabawa shugaba Tinubu da matarsa bisa goyon bayan da suke baiwa jama’a. (NAN) (www.nannews.ng)
Edited by Aisha Ahmed