ICRC ta kwashe mutane 117 daga cibiyoyin kiwon lafiya 4 a Maiduguri

ICRC ta kwashe mutane 117 daga cibiyoyin kiwon lafiya 4 a Maiduguri

Spread the love

 

ICRC ta kwashe mutane 117 daga cibiyoyin kiwon lafiya 4 a Maiduguri

Ficewa

Daga Franca Ofili

Abuja, Satumba 23, 2024 (NAN) Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce ta kwashe mutane 117 daga cibiyoyin kiwon lafiya hudu da ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Borno.

Aliyu Dawobe, jami’in hulda da jama’a na ICRC ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a ranar Litinin a Abuja.

Ya ce kungiyar ta kuma bayar da gudummawar jakankuna 150 ga hukumar NRCS, da asibitin kwararru na jihar da kuma hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar.

“ Madatsar ruwan Alau ta fashe ne da sanyin safiyar ranar 10 ga watan Satumba, abinda ya haddasa ambaliyar ruwa a Maiduguri.

“Kafin faruwar lamarin, ruwan sama kamar da bakin kwarya ya mamaye yankuna da dama a jihar lamarin da ya shafi hanyoyin shiga.

“Fiye da mutane 414,000 ne abin ya shafa tare da lalata gidaje da dama da amfanin gona.

“Akwai matukar damuwa ga fararan hula wadanda rikicin yankin ke cigaba da shafa,” in ji Dawobe.

A cewarsa, hadakar kungiyoyin agaji na ICRC da na NRCS ne ya shiga aikin bincike da ceton.

Ya ce sun kuma gudanar da aikin kwashe marasa lafiya tare da bayar da agajin gaggawa, da kuma hada kan iyalai da ambaliyar ruwa ta raba su da kuma kula da gawarwaki cikin aminci.

“Kungiyoyin sun kwaso gawarwaki 22 zuwa yau, yayin da yara 76 suka koma ga iyalansu.

“An kwashe mutane 117 daga cibiyoyin kiwon lafiya hudu da ruwan ya shafa.

“Hukumar ICRC ta kuma ba da gudummawar jakunkuna 150 ga NRCS, Asibitin Kwararru na Jiha da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jiha (SEMA).

“NRCS ta kaddamar da ayyukan inganta tsafta a sansanoni uku da su ka karbi bakuncin al’ummomin da ambaliyar ruwa ta shafa tare da hadin gwiwar ICRC,” in ji Dawobe.

Dawobe ya ce a wani bangare na shirin rigakafin cutar kwalara, ICRC ta tanaji magunguna da suka hada AquaTabs da hodar chlorine don shirin ko ta kwana.

“Ana horar da masu aikin sa kai na NRCS kan yadda ake amfani da wadannan kayan kuma suna ba da fifiko wajen tsaftace rijiyoyi, famfunan hannu, rijiyoyin burtsatse, da sauran hanyoyin ruwa na al’umma.

“ICRC ta shirya zaman tallafi na zamantakewa don ma’aikatan NRCS da masu sa kai waɗanda suka shiga cikin ayyukan mayar da martani da yawa.

“A cikin kwanaki masu zuwa, ICRC tare da haɗin gwiwa tare da NRCS, za ta mika muhimman kayan gida ga gidajen da abin ya shafa, ciki har da taburmai, barguna, kayan dafa abinci, gidajen sauro, bokiti, sabulu, kayan tsaftacewa da tufafi, ” Yace.

A cewarsa, ICRC ta kuma taimaka wa Nijar, Kamaru da Chadi don magance matsalar ambaliyar ruwa.(NAN)( www.nannews.ng)

FNO/AMM

Fassara daga Nabilu Balarabe

=======

 


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *