Katsina ta mayar da ‘yan mata 42,781 makaranta ta hanyar shirin AGILE
Katsina ta mayar da ‘yan mata 42,781 makaranta ta hanyar shirin AGILE
‘Yan mata
Daga Abbas Bamalli
08032970758
Katsina, Yuli 23, 2025 (NAN) Akalla ‘yan mata 42, 781 ne gwamnatin jihar Katsina ta mayar da su makaranta, ta hanyar shirin ‘yan mata masu tasowa don koyon karatu da karfafawa (AGILE).
Dokta Mustapha Shehu, Ko’odinetan AGILE a jihar ne ya bayyana hakan a taron wayar da kan al’umma na kwana daya da aka gudanar a Katsina ranar Talata.
Yakuwar na da taken “Ƙarfafa Tallafin Al’umma don Ilimin ‘Yan mata ta hanyar Tallafin Kuɗi (CCT)”.
Shehun ya bayyana cewa an samu nasarar ne cikin kimanin shekaru biyar, tun da aka fara aikin a jihar.
Ya kara da cewa a cikin wannan lokaci, ta hanyar rukunin farko, na biyu da na uku, aikin ya inganta tattalin arzikin gidaje kusan 115,568.
Ya bayyana cewa bayar da tallafin ga iyaye kasa da 48, 000 da ‘yan mata 43,000 ta hanyar tallafin karatu ya fara ne a rukuni hudu na shirin.
A cewar kodinetan, makasudin taron shi ne wayar da kan jama’a domin su kara sanin bangaren CCT na shirin da yanayinsa da kalubalen da ke fuskanta.
“Taron da nufin tattaunawa, musayar ra’ayi da shawarwari, ta yadda za a inganta shirin. Tuni muna da cibiyoyin korafe-korafe a fadin jihar.”
Ya kara da cewa, a yanzu haka an samu katinan ATM sama da 2,900 da aka yiwa rijistar tallafin CCT, inda ya nuna cewa mutane sun kasa karban su saboda ba su ne suka ci gajiyar kudin ba.
“Lokacin da muke yiwa daliban firamare shida rajista, muna fatan za su koma kananan sakandare, daya daga cikin makarantun da suka ci gajiyar shirin ta yanke shawarar shigar da yaran firamare biyar.
“A karshen wa’adin, mun ziyarci makarantar sakandare inda ake sa ran yaran za su wuce, ba mu same su ba, amma da muka dawo makarantar firamare, mun gansu a firamare shida,” in ji shi.
Shehu ya bayyana cewa an bullo da AGILE ne a Katsina bayan wani bincike da aka gudanar a shekarar 2019, da 2020, wanda ya nuna cewa kashi 53 na daliban firamare ba sa komawa karamar sakandare.
Ya kara da cewa binciken ya nuna cewa kashi 43 cikin 100 ba sa wucewa daga zuwa babbar sakandire, kuma yawancinsu ‘yan mata ne.
“Binciken ya kuma nuna cewa rashin isassun makarantu na daya daga cikin abubuwan da ke haifar da hakan, domin a wasu wuraren yara kan yi tafiyar kilomita 10 don zuwa makaranta.
“Tsarin mulkin Najeriya ya ce daliban firamare kada su yi tafiyar kilomita biyar kafin su je makaranta, yayin da yaran sakandare kuma ba za su yi tafiyar kilomita bakwai ba.
“Rahoton ya kuma nuna cewa yawancin makarantun da ake da su sun lalace, sannan kuma talauci ya taimaka wajen rashin samun sauyi,” in ji shi.
Ko’odinetan CCT na aikin, Dokta Kubrah Muhammad, ta ce aikin da bankin duniya ya taimaka ya mayar da hankali ne kan inganta guraben karatun sakandare ga ‘yan mata masu tasowa a jihohin da aka yi niyya.
A cewarta, shirin na da nufin kara wa ‘ya’ya mata rijista, darewa da kuma kammala karatun sakandare, tare da kara musu kwarin gwiwa da dabarun rayuwa.
Ta kara da cewa muhimman abubuwan da suka shafi aikin sune, inganta kayayyakin makarantu, gyara ajujuwa da samar da wuraren koyo lafiya.
Muhammad ta kuma ce aikin yana bayar da tallafin kudi, bayar da tallafin karatu da CCT ga ‘yan matan da suka cancanta da iyalansu. (NAN) (www.nannews.ng)
AABS/DCO
====
Deborah Coker ne ya gyara shi