All posts by Hadiza Mohammed-Aliyu

Tinubu zai tafi ƙasar Sin don ziyarar aiki

Ziyara
Daga Salif Atojoko
Abuja, Agusta 29, 2024 (NAN) Shugaban Kasa Bola Tinubu zai bar Abuja zuwa Beijing, Kasar Sin, a ranar Alhamis don ziyarar aikin gwamnati da ta shafi Kasa da Kasa.

Jami’in yada labarai na fadar Shugaban Kasa, Ajuri Ngelale, ya bayyana cewa Tinubu zai yi aiki na ɗan lokaci a Kasar Gamayyar Larabawa (United Arab Emirates) .

Ya kara da cewa “a kasar Sin, Shugaban kasar zai gana da Shugaba Xi Jinping na Kasar Sin kuma ya yi ganawa da shugabannin kasuwancin kasar Sin a kan batun taron hadin kai tsakanin Kasar Sin da yankin Afirka.

“A cikin tawagar akwai jami’an gwamnatin tarayya tare da wasu muhimman mutane da su ka marawa Shugaba Tinubu baya a tafiyar.” (NAN)(www.nannews.ng)

SA/BRM
=======
Bashir Rabe Mani ne ya buga

Muna neman taimakon gwamnati – Masu ciwon sugar

Muna neman taimakon gwamnati – Masu ciwon sugar

Muna neman taimakon gwamnati – Masu ciwon sugar

Taimako
Daga Christian Njoku
Calabar, Aug. 29, 2024 (NAN) Wata kungiya mai suna — National Association of Persons Living with Diabetes – tayi kira ga gwamnatin tarayya da ta taimaka wa masu cutar sugar saboda kudin abinci da magani sun hau.

Kungiyar tayi kiranne a wata hira da Mr Bernard Enyia, mai kula da harkar kungiyar yayi da kamfanin dillancin labarai na Nigeria (NAN) ranar alhamis a Calabar.

Enyia yace da yawa daga cikin masu fama da cutar sun rasa wayukansu saboda rashin kudin sayan magani da wadataccen abinci.

Ya kara da cewa dayawa a cikin masu fama da ciwon sun koma ga maganin gargajiya saboda bazasu iya sayan maganin asibiti ba.

Yace yawancin maganin ciwon sugar sai an kawosu ne daga kasashen ketare, shi yasa suke tsada, sai ya bukaci gwamnati da ta tallafa wa al’umma.

Enyia ya kara da cewa kudin alluran insulin da masu cutan suke amfani dashi wanda yake yi musu sati daya kacal, ya haura zuwa N19,000 ko N24,000 daga N4000 da suke saye a 2022.

Mai kula da al’amuran kungiyan yace har farashin alluran syringe da masu cutar suke amfani dashi ya hau daga N50 zuwa N600, kuma ana bukatar ayi anfani da guda biyu a kowane rana.

Yace masu cutar sugar suna cikin mawuyacin hali, sai ya nemi taimakon gwamnati da sauran al’umma wajen tabbatar da sun samu magani cikin sauki.(NAN)(www.nannews.ng)
CBN/HA
========
Hadiza Mohammed-Aliyu ce ta tace