Shugaba Tinubu ya raba tallafin taki da shinkafa ga marasa galihu a Gombe
Shugaba Tinubu ya raba tallafin taki da shinkafa ga marasa galihu a Gombe
Kyauta
Daga Hajara Leman
Gombe, Agusta 29, 2024 (NAN) Shugaban kasa Bola Tinubu, a ranar Laraba ya bayar da gudummawar tireloli guda biyu kowannen cike da shinkafa da taki ga marasa galihu a jihar Gombe.
Alhaji Saidu Alkali, Ministan Sufuri ne ya raba kayan a madadin Shugaba Tinubu.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN, ya ruwaito cewa motocin taki da shinkafa kowanne yana dauke da buhu 1,200.
Da yake jawabi a wajen taron, Alkali ya ce shugaban kasar ya yi hakan ne da nufin rage wahalhalun da masu karamin karfi ke fuskanta.
A cewar ministan, wannan karimcin wata shaida ce ta alherin da Tinubu ke nunawa al’ummar Gombe, da ya ke rike da zuciyarsa.
Da yake karbar kayayyakin a madadin gwamnatin jihar Gombe, wani dattijo kuma jigo a jam’iyyar All Progressives Congress (APC), a Gombe, Alhaji Abba Sadiq, ya nuna jin dadinsa ga shugaban kasa kan wannan karimcin.
Sadiq ya kara da cewa hakan zai taimaka matuka wajen bayar da gudunmawar bunkasa noma a jihar, da kuma tabbatar da samun isasshen abinci ga mutanen Gombe.
Ya kuma bai wa gwamnatin tarayya tabbacin cewa kayayyakin za su kai ga wadanda za su amfana. (NAN) (www.nannews.ng)
HUL/DOR
========
Nyisom Fiyigon Dore ta gyara
Shugaban Kasar Nijar yayi kira ga ‘Yan jaridu da su himmatu don cigaban Afrika
Shugaban Nijar yayi kira ga ‘Yan jaridu da su himmatu don cigaban Afrika
Kungiya
Daga Muhammad Nasir
Niamey (Kasar Nijar) Agusta, 26, 2024 (NAN) An kalubalanci ‘Yan jaridu masu amfani da harshen Hausa da su himmatu wajen hana yaduwar labarin bogi, dabbaka dajarajar da ci gaban Afrika.
Shugaban Kasar Niger, Brig.-Gen. Abdourahmane Tchiani, ya yi kiran ne a lokacin taron tattaunawa na kwana uku da kaddamar da qungiyar ‘yanjarida masu amfani da harshen Hausa a babban birnin Yamai.
Tchiani ya ce ‘yanjaridu sune idanun al’umma da kuma masu shiga tsakanin mahukunta jagororin gwamnati da al’ummar da a ke mulka.
Shugaban kasar wanda Friministan kasar, Ali Lamine-Zeine, ya wakilta ya jinjinawa ‘yanjaridu na Afrika wajen ayyukansu kuma ya qara kira garesu da su himmatu wajen daukaka darajar kasashen su da Afrika gabadaya.
Bako da mussamman a wajen taron, Manjo Hamza Al’Mustafa murabus, kuma tsohon dogarin Shugaban mulkin Soja na Nijeriya, Marigayi Janar Sani Abacha, ya yabawa kasar Nijar wajen kammala taron.
Al’Mustafa ya yi kira ga ‘Yanjaridu su himmatu wajen karfafa kasashen su ta hanyoyi daban da suka hada da tattalin arziki, ilmi, lafiya da zaman lafiya don ci gana kasashen.
” Muna kira ga kasashen mu na Afrika mu himmatu wajen zakulo ma’adananmu, noma da kiyo da sauran harkokin tattalin arziki don ci gaban mu, ” Al’Mustafa ya yi kira
Da take magana bayan kaddamar da kungiyar, shugaba ta farko, Hajiya Mariama Sarkin-Abzin, ta yaba kazon himmar ‘yanjaridun masu aiki da harshen Hausa Kuma ta yi kira da su kara jajircewa a ayyukansu.
Sarkin-Abzin ta ki kira ga ‘Yanjaridu su kara himmatuwa wajen samun ‘yancin ‘aikin ‘yanjarida, walwala da fadin albarkatun baki.
Kamfanin Dillancin Labarin Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa mahalarta taron sun fito daga kasashen; Nijeriya, Nijar, Chadi, Mali, Burkina Faso, Sudan, Benin, Togo, Ghana, Kamaru da Côte d’Ivoire. (NAN) (www.nannews.ng)
BMN/
======
Tace wa: Bashir Rabe Mani