APC da PDP su na kalubalantar sake zaben Adeleke a jihar Osun

APC da PDP su na kalubalantar sake zaben Adeleke a jihar Osun

Spread the love

APC da PDP suna kalubalantar sake zaben Adeleke a jihar Osun

Zaɓe
Daga Joshua Oladipo
Osogbo, Satumba 7, 2026 (NAN) Jam’iyyun All Progressives Congress (APC) da Peoples Democratic Party (PDP) sun shigar da ƙara a gaban Kotun Ƙorafe-ƙorafen Zaɓen Gwamnan Osun suna ƙalubalantar sake zaɓen Gwamna Ademola Adeleke.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa an liƙa ƙarar a kan allon sanarwa na sakatariyar kotun da ke Osogbo a ranar Litinin.

NAN ta kuma ruwaito cewa ƙarar ta nuna fara aikin shari’a da ya taso daga zaɓen gwamna na ranar 15 ga Agusta wanda a ka ayyana Adeleke ya zama wanda ya yi nasara.

Sakataren kotun, Mista Pete Belemore, ya tabbatar wa NAN cewa jam’iyyun siyasa biyu na adawa sun shigar da ƙarar da ke ƙalubalantar sakamakon zaɓen a gaban kotun.

Belemore more ya ce za a sanar ranar fara sauraron karar ran da ta dace a kan allon sanarwar kotun kafin ƙarshen yau (Litinin).

Ya ce ci gaban ya share fagen aika wa waɗanda ake ƙara a cikin ƙarar a hukumance da kuma fara shari’o’in da za su biyo baya.

A cewarsa, ana sa ran kotun za ta saurari koke-koke bisa ga tanade-tanaden Dokar Zabe da sauran dokokin da suka shafi kararrakin zabe.

NAN ta kuma ruwaito cewa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta ayyana Adeleke na Accord a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 15 ga Agusta, bayan ya kayar da abokin hamayyarsa mafi kusanci, Mista Bola Oyebamiji, na APC. ( NAN )
JOO/WAS
An gyara ta ‘Wale Sadeeq


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *