Sabon Shugaban asibitin kwakwalwa ya bukaci ma’aikata su tabbatar da ingantaccen aiki ga marasa lafiya

Sabon Shugaban asibitin kwakwalwa ya bukaci ma’aikata su tabbatar da ingantaccen aiki ga marasa lafiya

Sabon Shugaban asibitin kwakwalwa ya bukaci ma’aikata su tabbatar da ingantaccen aiki ga marasa lafiya

Spread the love

Sabon Shugaban asibitin kwakwalwa ya bukaci ma’aikata su tabbatar da ingantaccen aiki ga marasa lafiya 

Ayyuka
Daga Habibu Harisu
Kware (Jihar Sokoto), Dec. 5, 2025 (NAN) Dr Sulaiman Baguda, sabon Daraktan lafiya na Asibitin Kula da tabin hankali na Gwamnatin Tarayya (FNPH) da ke Kware a Jihar Sakkwato, ya hori ma’aikata da su samar da ingantattun ayyuka ga ‘yan kasa.
Ya yi kiran ne a ranar Juma’a yayin ganawarsa ta farko da ma’aikatan asibiti bayan ya zama babban daraktan kula da lafiya.
Ya bayyana kwarewa a matsayin mafi kyawun kayan aiki na samun nasara sannan ya bukaci ma’aikata su inganta kansu da fasahar zamani a sassansu.
Ya kuma bukaci shugabannin ma’aikatu da su yi aiki da sauran ma’aikatan da ke karkashinsu, inda ya jaddada cewa duk abin da ya faru a cikin sassansu na nuni ne da irin aikin da suke da shi.
Baguda ya bukaci ma’aikatan da su tashi tsaye  don fuskantar duk kalubale a wuraren aikin su, yana mai cewa asibitin zai ci gaba da zama wurin samar da kiwon lafiya mai inganci.
Ya kuma ba su tabbacin bayar da cikakken goyon bayansa a kowane lokaci domin asibitin ya zarce nasarorin da yake samu a yanzu ta hanyar gudanar da ayyuka masu ma’ana.
“Wannan shi ne don daidaita ra’ayoyi da  za su haifar da ingantaccen sauye-sauye masu tasiri kan yadda cibiyar ke ba da sabis na kiwon lafiya ga ‘yan Najeriya.
“Asibitin yana aiki ne a matsayin na bincike mai zurfi, fagen horo kuma yana ba samar da kiwon lafiya ga kowane nau’in mutane, musamman kula da lafiyar hankali.
“Muna da ma’aikata na musamman, ingantattun wurare da kayan aiki, gudanar da bincike, jiyya da sauran kulawa na musamman,” in ji Baguda.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Baguda, wanda tun farko yana kan mukamin wucin gadi, shugaban kasa Bola Tunubu ya tabbatar da shi a matsayin babban daraktan kula da lafiya a watan Nuwamba.(NAN)( www.nannews.ng )
HMH/HA
=======
Hadiza Mohammed-Aliyu ta gyara

Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *