Zaben kananan hukumomin Jihar Kebbi: Al’umma sun bijirewa ruwan safe su na kada kuri’u
Zaben kananan hukumomin Jihar Kebbi: Al’umma sun bijirewa ruwan safe su na kada kuri’u
Mata masu zabe, suna kada kuri’a duk da ruwan sama kamar da bakin kwarya a makarantar firamare ta Magajin Gari Model Primary, a mazabar Marafa.
Zaben kananan hukumomin Jihar Kebbi: Al’umma sun bijirewa ruwan safe suna kada kuri’u
Zabe
Daga Ibrahim Bello
Birnin Kebbi, Aug. 31, 2024 (NAN) Masu zabe a jihar Kebbi sun bijire wa ruwan safe sun fito domin kada kuri’unsu a zaben kananan hukumomi da ke gudana, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito.
Binciken da wakilin NAN ya gudanar a rumfunan zabe daban-daban a babban birnin jihar, Birnin Kebbi, ya nuna cewa fitowar jama’a domin gudanar da zabubbukan ya kayatar matuka, bisa la’akari da ruwan sama mai karfi da a ke yi tun daren Juma’a wanda ya kai har safiyar Asabar.
NAN ta kuma ruwaito cewa an gudanar da tantancewa da kada kuri’a a lokaci daya bisa ka’idojin da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kebbi (KESIEC) ta fitar.
A Birnin Kebbi jami’an zabe sun isa rumfunan zabe kafin karfe 8:30 na safe. tare da muhimman kayan zabe a mafi yawan rumfunan zabe.
Ma’aikacin hukumar zabe ta a mazabar Garkar Magatakarda dake unguwar Tudun-Wada a Birnin Kebbi, Malam Yanusa Shehu, ya ce jami’an hukumar ta KESIEC sun isa ne kafin karfe 8:30 na safe.
“Mun samu ɗimbin fitowar jama’a kuma masu jefa ƙuri’a har yanzu suna fitowa don kada ƙuri’unsu,” in ji shi.
Ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu babu wata tangarda duk da cewa an gudanar da aikin ne da hannu da kuma tsarin kada kuri’a viking sirri, inda ya kara da cewa masu zabe sun kasance cikin tsari da lumana.
A unguwar Marafa 004 da ke Baiti Liman Poling Unit a Birnin Kebbi, masu kada kuri’a sun yi jerin gwano domin gudanar da ayyukansu na al’umma.
Jami’an hukumar zaben sun isa da karfe 7:30 na safe. a mazabar Magawata da ke unguwar Marafa, Birnin Kebbi, yayin da a ka fara tantancewa da kada kuri’a da misalin karfe 9:00 na safe ba kamar yadda KESIEC ta tanada ba.
Da karfe 9:35 na safe ne kuma a ka fara kada kuri’a a mazabar Mai-Alelu dake unguwar Nasarawa ta 2, inda a ke sa ran ministan kasafin kudi da tsare-tsare na tattalin arziki, Atiku Bagudu zai kada kuri’arsa.
Wasu masu kada kuri’a a Dangaladima, 003, Dangaladima Ward, Shehu Zalaka 004, Gorabu da Zoramawa ward sun bayyana jin dadinsu da fara zaben da karfe 8:30 na safe ba tare da bata lokaci ba.
Sai dai kuma masu kada kuri’a a mazabar Nasarawa mai lamba 002 da ke unguwar Nagari College Ward, Birnin Kebbi, duk da cewa jami’an zabe sun fito da wuri, sai daga baya masu kada kuri’a suka fara fitowa.
Yayin da aka fara tantancewa da kada kuri’a da karfe 8:30 na safe, fitowar masu kada kuri’a kuma ya burge sosai.
A rumfar zabe ta Makeran Gwandu 007, Kwalejin Nagari inda a ke sa ran Gwamna Nasir Idris zai kada kuri’a, jami’an zaben sun isa da karfe 8:00 na safe.
Malam Umar Yalli, Shugaban Hukumar KESIEC, ya ce an fara kada kuri’a ne da karfe 8:30 na safe kamar yadda tsarin zabe da zaben KESIEC ya tanada.
“Muna ganin ana gudanar da zaben ba tare da cikas ba da kuma tantancewa da kada kuri’a a lokaci guda.
“Masu kada kuri’a sun fito gadan-gadan amma saboda ruwan sama ya sa suka fita domin fakewa da zarar sun kada kuri’a,” inji shi. (NAN) (www.nannews.ng)
IBI/KLM/HMH
============
Muhammad Lawal ne ya gyara