Wata kungiyar bada tallafi ta kaddamar da aikin tiyatar gyaran jiki kyauta a Sokoto
Wata kungiyar bada tallafi ta kaddamar da aikin tiyatar gyaran jiki kyauta a Sokoto
Tiyata
Daga Habibu Harisu
Sokoto, Satumba 8, 2025 (NAN) A ranar Litinin din da ta gabata ne gidauniyar Kindred Health Surgical Foundation ta kaddamar da wani shirin tiyata na sake gina sassan jiki kyauta ga marasa galihu 30 a jihar Sokoto.
Farfesa Jacob Legbo, Likitan Filastik da Gyaran jikii na Jami’ar Usmanu Danfodio Teaching University Sokoto (UDUTH) ne ya bayyana haka a wajen taron wayar da kan jama’a da aka gudanar a Sakkwato.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa Gidauniyar ce ta shirya shi tare da hadin guiwar wani Likitan kunne na Amurka Dokta Dave Shaye a karkashin gidauniyar Project Life Foundation.
NAN ta ruwaito cewa tawagar kwararrun likitocin fida, kwararrun likitoci, da masu aikin sa kai za su gudanar da ayyukan ceton rai kyauta daga ranar 8 ga watan Satumba zuwa 12 ga watan Satumba a asibitin kwararru na Noma dake Sokoto.
Legbo, wanda shi ne shugaban tawagar, ya ce kungiyar ya mayar da hankali ne wajen bayar da tallafi ga marasa lafiya.
“Muna gudanar da aikin tiyata kyauta ga marasa lafiya wadanda ba za su iya biyan kudin aikin tiyata ba kuma wadanda suka ci gajiyar aikin sun fito ne daga sassan Najeriya.
“Wadannan ayyukan za su rage radadi kai tsaye ga marasa galihu, mutanen da ke da nakasa a kan yanayin barazanar rayuwa da ke addabar mutane da yawa a cikin al’ummominmu.
“Tallafin ya kuma hada da marasa lafiya da ke karkashin magunguna na yau da kullun a wasu asibitoci, duk an yi niyya ne don ba da tallafi ga mutane da iyalansu,” in ji Legbo.
A cewarsa, zagayen tiyata guda daya yana Iya kai Naira 350,000 zuwa Naira miliyan 1 a asibitin koyarwa. Wasu marasa lafiya suna buƙatar maimaita tiyata a wasu lokuttan.
Legbo ya lura cewa bayan shirin dakunan tiyata, shirin zai kuma mai da hankali kan ilimin marasa lafiya, kulawa bayan tiyata, da horar da likitocin mazauna wurin zama likitocin tiyata tare da kwararrun likitocin cikin gida don tabbatar da tsarin kiwon lafiya mai dorewa.
Ya bayyana cewa a karkashin wannan shiri gidauniyar za ta samar da kayan aikin tiyata ga wasu wurare da kuma wasu abubuwan da ake bukata.
“A halin yanzu, muna mai da hankali kan aikin tiyata na musamman na kai da wuya don ENT, da na musamman na filastik da tiyata.
Ya kara da cewa, “Muna sa ran fadada aikin atisayen bisa la’akari da tallafin shiga tsakani yayin da ake gano masu rauni a cikin al’umma,” in ji shi.
Wani bangare na iyalai da suka amfana sun yaba da matakin da kungiyar ta yi, inda suka bayyana ta a matsayin ceton rayuka, tare da bayyana cewa da yawa ba sa iya biyan kudin magani musamman a yankunan karkara. (NAN)(www.nannewa.ng)
HMH/ADA
Deji Abdulwahab ne ya gyara
=====