Tsarin Hajjin adashen gata shi ne mafi kyawun zaɓin biyan kudin Hajji mai nasara – Farfesa Yagawal

Tsarin Hajjin adashen gata shi ne mafi kyawun zaɓin biyan kudin Hajji mai nasara – Farfesa Yagawal

Tsarin Hajjin adashen gata shi ne mafi kyawun zaɓin biyan kudin Hajji mai nasara – Farfesa Yagawal

Spread the love

Tsarin Hajjin adashen gata shi ne mafi kyawun zaɓin biyan kudin Hajji mai nasara – Farfesa Yagawal

Tattalin Arziki
Daga Habibu Harisu
Sokoto, Nuwamba 24, 2025 (NAN) Tsarin Hajjin adashen gata shi ne mafi kyawun hanyar biyan kudin Hajji don samun cikkakiyar nasarar aikin Hajjin.

Farfesa Abubakar Yagawal, Kwamishinan Tsare-tsare, Bincike, Kididdiga, Watsa Labarai da Laburare (PRSILS) a Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON), ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN a ranar Litinin a Sokoto.

NAN ta ruwaito cewa shirin, hadin gwiwa tsakanin NAHCON da bankunan da ba bashi mai ruwa, musamman bankin Jaiz , ya baiwa mahajjata damar yin tanadi na tsawon lokaci ta hanyar da ta dace da Shari’a. 

Ya bayyana fatansa cewa tsarin zai hana jinkirin biyan kudin aikin Hajji ta hanyar niyya da wuri ga mahajjata, da samar da wuraren kwana a wurare masu kyau a Makka da Madina tare da tabbatar da tsare-tsare masu inganci.

Ya koka da yadda jinkirin biyan kudin aikin Hajji ya haifar da bada lokacin shirye-shirye, tare da samar da matsuguni a wurare masu nisa yana mai jaddada cewa mahukuntan Saudiyya na tabbatar da shirye-shiryen wanda ya fara zuwa.

“Mafi yawan ’yan Najeriya suna jira har wa’adin da aka kayyade don biyan kudin ya kusa cika, wasu su garzaya don sayar da dabbobinsu ko amfanin gonakinsu su biya kudi a lokaci daya, kashi biyu ko uku.

“Halayen na kawo cikas ga gudanar da shirye-shirye a Najeriya ba tare da wata matsala ba, saboda a kullum mahukuntan Saudiyya suna tattaunawa da kasashen duniya kan aikin Hajjin bana mai zuwa nan da nan bayan kammala ibadar shekara guda.

“Akwai bukatar a fahimci cewa Hajji ibada ce ta rayuwa da ke bukatar tsari na tsawon shekaru,” inji shi.

Yagawal ya bayyana cewa tsarin adashen gata na bada damar tsari mai kyau, kuma aikin Hajji abu ne na duniya wanda ke baiwa hukumomin jin dadin alhazai damar tsara aikin hajji na shekaru.

A cewarsa, mahajjaci zai iya tuntubar wata cibiyar hada-hadar kudi da aka kebe tare da tsarin adashen gata aikin Hajji don ajiya wanda yawanci ana raba shi a cikin kaso kaso.

“Tsarin na tabbatar da rage kudin aikin Hajji ga maniyyata saboda kudaden da mahajjaci ya ajiye a bankuna za su kasance bisa halaltacciyar mu’amala ta hanyar amfani da kudaden, ta yadda mai shi zai amfana da kudaden da doka ta tanada.

“Wannan tsari ne wanda za a yi gada da zai tanadin hidimomi da tsararraki masu zuwa, musamman don matasa da masu karamin karfi,” in ji Yagawal.

Ya yabawa shugaban kasa Bola Tinubu bisa jajircewarsa na ganin an gudanar da aikin Hajji cikin sauki, da kuma bada damar gudanar da aikin Hajji kan tsari Mai kyau tare da samun karin nasarori tare da amincewa da rage farashin maniyyata aikin hajjin 2026 a halin yanzu.

Yagawal ya kuma yabawa Gwamnonin Jihohin bisa irin tallafin da suke baiwa Hukumar NAHCON musamman kungiyar Gwamnonin Arewa Maso Yamma bisa shirinsu na ganin an biya su.

Yagawal ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su yi taka tsantsan wajen kiyaye wa’adin da hukumomin Saudiyya suka kayyade don gudanar da aikin Hajji na 2026.

NAN ta ruwaito cewa an kafa tsarin adashen gata na aikin Hajji ne bisa ka’idar Mudaraba (partnership), inda ake zuba jari da ribar da ake samu tare da raba wa masu ajiya, wanda hakan zai taimaka wajen bayar da tallafin kudin Hajji.

An tsara tsarin ne ga dukkan musulmi ba tare da la’akari da kuɗin shiga, shekaru, ko matsayinsu ba.

Mahajjata za su iya buɗe asusu tare da lambobin (BVN da NIN) kuma su zaɓi tsarin biyan kuɗi mai sauƙi (kullum, mako-mako, kowane wata, kwata, ko shekara-shekara.( NAN)( www.nannews.ng )

HMH/SH

=======
Sadiya Hamza ta gyara

=====


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *