Tinubu ya ta’aziyyar malamin addinin musulunci, Sheikh Modibo Daware

Tinubu ya ta’aziyyar malamin addinin musulunci, Sheikh Modibo Daware

Spread the love

Tinubu ya ta’aziyyar malamin addinin musulunci, Sheikh Modibo Daware

Makoki

By Salif Atojoko

Abuja, 10 ga Fabrairu, 2025 (NAN) Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana alhininsa kan rasuwar Shahararren malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Modibbo Daware daga Adamawa.

Daware ya kasance shugaban darikar Tijjaniyya da ake mutuntawa wanda ya kwashe tsawon rayuwarsa yana koyar da ilimi, jagoranci da kuma tsara tunanin mutane da dama, in ji shugaban a wata sanarwa da Mista Bayo Onanuga, kakakinsa ya fitar.

Tinubu ya yaba da irin tawali’u da tsoron Allah da sadaukarwar Daware wajen neman ilimi tare da bayyana mutuwarsa a matsayin rashi mai zafi ba ga iyalansa da al’ummarsa kadai ba har ma da kasa baki daya.

“Ina mika ta’aziyyata ga gwamnatin jihar Adamawa, da iyalan marigayi malamin, da mabiyansa.

“Allah Ya jikansa da rahma ameen.

Shugaban ya kara da cewa, ” Abinda mamacin Sheikh Daware ya bari zai ci gaba da kara mana kwarin gwiwa, tare da tunatar da mu tasirin imani, ilimi, da kuma sadaukar da kai ga bil’adama.” (NAN) (www.nannews.ng)

SA/BRM

=========

Edited by Bashir Rabe Mani


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *