Tinubu ya nuna jimamin rasuwar mahaifiyar marigayi shugaban kasa Yar’adua, Hajiya Dada

Tinubu ya nuna jimamin rasuwar mahaifiyar marigayi shugaban kasa Yar’adua, Hajiya Dada

Spread the love

Tinubu ya nuna jimamin rasuwar mahaifiyar marigayi shugaban kasa Yar’adua, Hajiya Dada

Makoki

Dgaa Salif Atojoko

Abuja, Satumba 2, 2024 (NAN) A ranar Litinin ne shugaban kasa Bola Tinubu ya jajantawa iyalan ‘Yar’aduwa bisa rasuwar Hajiya Dada.

Hajiya Dada, ita ce mahaifiyar marigayi tsohon shugaban kasa Umaru ‘Yar’aduwa, da kuma marigayi Janar Shehu ‘Yar’adua.

Marigayiyar ta rasu ne a daren ranar Litinin, kamar yadda mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale, ya fitar a wata sanarwa.

Tinubu ya kuma mika ta’aziyyarsa ga Sanata Abdulaziz Yar’adua, al’ummar Jihar Katsina, da dimbin rayukan da marigayiyar ta shafa.

“Shugaban kasa na jimamin Hajiya Dada, amma duk da haka yana daukaka abin da ta bari na tausayi, imani, gaskiya, da kyakkyawar zumunci.

“Shugaba Tinubu ya yi addu’ar Allah ya jikan ta ya kuma tabbatar da cewa za a rika tunawa da uwargidan ‘Yar’Adua saboda goyon baya, zaman lafiya, farin ciki da ta sa wa mutane da yawa,” in ji Ngelale. (NAN) (www.nannews.ng)

SA/YEN/

==============
Mark Longyen ne ya gyara shi

 

 


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *