Tinubu ya kare hutu, ya dawo Abuja Talata

Tinubu ya kare hutu, ya dawo Abuja Talata

Spread the love

Tinubu ya kare hutu, ya dawo Abuja Talata

Hutu
Daga Muhydeen Jimoh

Abuja, 16 ga Satumba, 2025 (NAN) Shugaban kasa Bola Tinubu ya kammala hutun sa kafin lokacin da
aka tsara kuma zai koma Abuja ranar Talata domin ci gaba da aikinsa.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Mista Bayo Onanuga, ya
fitar ranar Litinin a Abuja.

Tinubu ya tafi kasar Faransa ne a ranar 4 ga watan Satumba domin yin wani bangare na hutunsa na shekara,
tare da shirin farko tsakanin Faransa da Ingila.

Onanuga a cikin wata sanarwa ya ce hutun zai dauki kwanaki 10 na aiki.

A yayin zamansa a birnin Paris, shugaba Tinubu ya yi wata liyafar cin abinci ta sirri da shugaban Faransa Emmanuel
Macron a fadar Elysée.

Shugabannin biyu sun tattauna muhimman batutuwan hadin gwiwa, inda suka amince da karfafa alakar Najeriya da Faransa domin samun ci gaba tare da kwanciyar hankali a duniya.(NAN)(www.nannews.ng)
MUYI/SH
========

Sadiya Hamza ce ta gyara


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *