Tinubu ya isa kasar Sin domin ziyarar aiki

Tinubu ya isa kasar Sin domin ziyarar aiki

Spread the love

Tinubu ya isa kasar Sin domin ziyarar aiki

Shugaban kasar Nijeriya, Bola Tinubu, yayin da jami’an gwamnatin kasar Sin suka tarbe shi a birnin Beijing na kasar Sin ranar Lahadi


Ziyara

By Salif Atojoko

Abuja, Satumba 1, 2025 (NAN) Shugaban kasa Bola Tinubu ya isa birnin Beijing na kasar Sin domin ziyarar aiki ta kwanaki biyar.

A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale ya fitar, ya ce ya isa kasar Sin da misalin karfe 9:00 na safiyar Lahadin nan, kuma ya samu tarba daga wasu manyan jami’an gwamnatin kasar Sin.

Tinubu ya samu rakiyar gwamnoni da suka Jada da Babajide Sanwoolu, Sani Uba na jihohin Legas da Kaduna, da kuma mambobin majalisar ministocinsa.

Ana sa ran shugaban kasar zai gana da takwaransa na kasar Sin Xi Jinping, inda zai ziyarci manyan kamfanonin kasar Sin guda biyu, Huawei Technologies, da kuma hukumar kula da layin dogo ta kasar Sin (CRCC).

Ngelale ya ce “Wannan na da nufin cimma daya daga cikin manyan ajandar shugaban kasa, wato kammala aikin layin dogo daga Ibadan zuwa Abuja.”

Bayan haka, ya ce shugaban kasar zai gana da manyan jami’an gudanarwa na manyan kamfanoni 10 na kasar Sin tare da shuwagabannin su da ke karkashin kulawar kasar da yawansu  kaddarorinsu ya kai dala tiriliyan 3 a sassa daban-daban na tattalin arziki.

A cewarsa, bayan haka shugaban zai halarci taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka (FOCAC), inda shugabannin kasashen Afirka da dama za su tattauna da shugabannin kasar Sin kan wasu muhimman batutuwa. (NAN) (www.nannews.ng)

SA/JPE

=====

Joseph Edeh ne ya gyara shi


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *