Tinubu ya cika alkawuran da ya yi wa Arewa — Idris
Tinubu ya cika alkawuran da ya yi wa Arewa — Idris

Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Alhaji Mohammed Idris.
Alkawura
Daga Collins Yakubu-Hammer
Kaduna, Yuli 30, 2025 (NAN) Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Alhaji Mohammed Idris, ya ce shugaban kasa Bola Tinubu
ya cika mafi yawan alkawuran da ya yi wa Arewa, kuma zai yi fiye da haka.
Daga Collins Yakubu-Hammer
Kaduna, Yuli 30, 2025 (NAN) Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Alhaji Mohammed Idris, ya ce shugaban kasa Bola Tinubu
ya cika mafi yawan alkawuran da ya yi wa Arewa, kuma zai yi fiye da haka.
Idris ya bayyana hakan ne a ranar Talata lokacin da yake gabatar da shirin wayar tarho da harshen Hausa kai tsaye mai suna “Hannu Da Yawa” a gidan Rediyon Najeriya Kaduna da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya sanyawa ido.
Ya ce “kafin zaben shugaban kasa a 2023, Tinubu ya zo gidauniyar tunawa da Sir Ahmadu Bello inda ya yi wa Arewa wasu alkawuran tsaro, ilimi da noma.
“Gidauniyar ce ta gayyace mu zuwa taronsu na kwana biyu na tattaunawa kan hada-hadar gwamnati da ‘yan kasa mai taken ‘Samun Alkawuran
Zabe: Samar da Hadakar Gwamnati da Jama’a don Hadin Kan Kasa.
“A sani cewa a lokacin da ya ci zabe, Tinubu ya cika alkawuran da ya yi wa Arewa, ya nada mutane da yawa daga Arewa domin su yi aiki da
shi a gwamnatinsa.
“Sun hada da ministan tsaro, mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, babban hafsan tsaro, ministocin noma, harkokin mata, kiwon lafiya, fasaha, al’adu da tattalin arziki, ni kaina da sauran su; a gaskiya mun fi 60 daga arewa muna aiki tare da Tinubu.
“Shekaru biyu kenan da gwamnatinsa, kuma muna kan gidauniyar da ministoci sama da 20 da sauran su, don bayar da labarin duk alkawuran da aka cika da kuma wasu gagarumin nasarori da suka shafi Arewa kadai, har ma da kasa baki daya.”
Ministan ya ce an samu wasu bayanai na bata-gari cewa Tinubu ya mayar da Arewa baya, yana mai cewa, amma yau mun nuna mun ga irin wannan
labari ba gaskiya ba ne. A gaskiya ya yi wa Arewa kokari.”
Idris ya jaddada cewa tawagar za ta ci gaba da wayar da kan jama’a musamman na Arewa game da gagarumin nasarorin da gwamnatin Tinubu ta samu.
(NAN)(www.nannews.ng)
CMY/BRM
========
Bashir Rabe Mani ne ya gyara