Sokoto: Wamakko bai gaji N13bn daga Bafarawa ba, in ji – Tsohon Akanta na Jiha

Sokoto: Wamakko bai gaji N13bn daga Bafarawa ba, in ji – Tsohon Akanta na Jiha

Spread the love

Sokoto: Wamakko bai gaji N13bn daga Bafarawa ba, in ji – Tsohon Akanta na Jiha

Kudade
Daga Habibu Harisu
Sokoto, Satumba 19, 2024 (NAN) Alhaji Aminu Abdullahi, tsohon Akanta Janar na Jihar Sakkwato, ya ce tsohon Gwamna Attahiru Bafarawa bai bar Naira biliyan 13 a asusun gwamnatin jihar ba.
Da yake jawabi ga manema labarai a ranar Alhamis, Abdullahi ya musanta ikirarin da Bafarawa ya yi a lokacin da yake kaddamar da gidauniyarsa ta N1billion a ranar Laraba a Sokoto.
Ya ce bisa wannan ikirari, gwamnatin tsohon Gwamna Aliyu Wamakko ta wancan lokacin ta kafa kwamitin bincike wanda Alhaji Abdurrahman Namadina ya jagoranta, kuma babu inda aka gano wannan adadin kudin. 
” Kwamitin Namadina ya binciki dukkan asusun bankunan gwamnati na wancan lokacin tare da mika bayanan ga hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) a lokacin da aka wata shari’a mai tsawo.
” Babban asusu na UBA a lokacin yana dauke da kudi miliyan N254. 5, har a ranar 29 ga Mayu, 2007 yayin da an samu miliyan N7. 3, a asusun gwamnatin jihar na VAT,” in ji Abdullahi.
Ya bayyana cewa Gwamna Wamakko na wancan lokacin ya dakatarda gudanar da hulda a duk wani asusu na banki da su ka kai guda 27 na gwamnatin Bafarawa kuma duk an rufe su ne saboda an gurfanar da su a gaban kotu a lokacin.
“Ya kamata duk wani mai hankani ya san cewa an tabbatar da ikirarin Bafarawa karya ne domin Kotu ta yanke hukunci kan lamarin,” inji shi.
Abdullahi ya ce wannan ikirari na Bafarawa ba shi da tushe balle makama, yana yaudarar jama’a ko kuma kawai da hankukansu don kawai a yi amfanin siyasa domin taso da batun shekara Sha bawai da ta wuce wani Abu ne daban.
“Har yanzu tambayar ta kasance na a amsa ba itace, a wane asusu ne Naira biliyan 13 su ke, kamar yadda muka bayar da dukkan lambobin asusun banki da bayanai, shi tsohon Gwamna akwai  bukatar da yayi cikakken bayani,” in ji tsohon Akanta Janar.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa Bafarawa ya yi aiki tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007 yayin da Wamakko ya mulki jihar a tsakanin shekarar 2007 zuwa 2015, yayin da dukkansu suka yi wa’adi biyu a jere. (NAN) (www.nannews.com)
HMH/BRM
============
Edited by Bashir Rabe Mani

Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *