Sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 1,166, sun kama mutane 1,096 da a ke zargi – Hukumar Tsaro
Sojoji
Sumaila Ogbaje
Abuja, Aug. 29, 2024 (NAN) Babbar rundunar tsaron aikin sojoji ta kasa ta ce sojoji sun yi nasarar kawar da ‘yan ta’adda 1,166, tare da cafke mutane 1,096 da ake zargi da aikata laifukfuka a cikin kwanaki 29 a fadin kasar nan.
Shugaban yada labarai na hukumar, Manjo Janar. Edward Buba, ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan ayyukan rundunar a ranar Alhamis a Abuja.
Buba ya ce sojojin sun kuma ceto mutane 721 da aka yi garkuwa da su.
Ya ce sojojin sun kuma kwato makamai 391, alburusai 15,234 da suka hada da bindigogi kirar AK47 guda 208, bindigogi kirar gida guda 54, bindigogin toka guda 53, bindigogi masu feshi 36, da kuma alburusai 10,452 ma tsawon mita 7.62 na musamman a cikin watan.
Sauran makaman a cewarsa, sun kunshi harsashi 1,991 na NATO masu tsawon mita 7.62, harsashi 293, makamai iri-iri 42 da harsasai iri daban daban su ka Kai guda 2,498.
Ya ce an kashe wasu shugabannin ‘yan ta’adda da kwamandoji a lokutan artabun sakamakon farmakin da sojoji suka kai musu a cikin watan.
A cewarsa, wadanda a ka kashe a Arewa maso gabas sun hada da: Munir Arika, Sani Dilla ( da a ka fi sani da Dan Hausawan Jibilarram), Amir Modu, Dan Fulani Fari Fari, Bakoura Araina Chikin, Dungusu, Abu Darda da Abu Rijab.
“Wadanda ke yankin Arewa maso Yamma sun hada da; Kachalla Dan Ali Garin Fadama, Kachalla Dan Mani Na Inna, Kachalla Basiru Zakariyya, Sani Baka Tsine, Inusa Zangon Kuzi, Ibrahim, Tukur da Kamilu Buzaru, da sauransu.
“Ayyukan da ake ci gaba da gudanarwa a duk fadin kasar sun yi matukar rage karfin kungiyoyin ta’addanci tare da hana ‘yan ta’adda damar kai gaggarumin farmaki.
“Halin da a ka fuskanta galibi a kwanakin nan shi ne fadace-fadace da kai hare-hare kan wurare masu sauki.
“Muna sane da cewa muna tunkarar abokan gaba masu wayo, marasa tausayi da muguwar dabi’a wadanda dole ne a dakatar da su daga ayyukansu na ta’addanci.
“Saboda haka, sojoji a shirye suke su yi aiki da daukar matakin da ya dace da za a yi don wargaza wadannan kungiyoyin ta’addanci.
“Dabarun sojoji shi ne su lalata karfin wadannan kungiyoyin ta’addanci da samar da yanayin da ba za su iya aiwatar da ayyukan ta’addanci ko cutar da mutanen kasa ba.
“Saboda haka, sojoji sun ba da fifiko wajen kai hari ga shugabannin ‘yan ta’adda, kwamandoji, sojojin kafa da kuma abokan aikinsu,” in ji shi.
A yankin Arewa maso gabas, Buba ya ce dakarun Operation Hadin Kai, sun kashe ‘yan ta’adda 292, sun kama mutane 254 da ake zargi da kuma ceto mutane 213 da aka yi garkuwa da su a cikin watan.
Ya kara da cewa wani adadin mayakan na Boko Haram/ISWAP 2,742 da iyalansu, sun mika wuya ga sojoji tare da kwato manyan makamai da alburusai.
A yankin Arewa ta tsakiya, Buba ya ce dakarun Operation Safe Haven sun kashe ‘yan ta’adda 50, sun kama 290 tare da kubutar da masu garkuwa da mutane 121 tare da kwato tarin makamai.
A karkashin Operation Whirl Stroke, ya ce sojojin sun kashe ‘yan ta’adda 37, sun kama mutane 94 da a ke zargi, tare da kubutar da mutane 68 da a ka yi garkuwa da su.
A yankin Arewa maso Yamma, kakakin rundunar tsaron ya ce dakarun Operation Hadarin Daji sun kashe ‘yan ta’adda 153, sun kama mutane 97 da a ke zargi da kuma kubutar da masu garkuwa da mutane 186 tare da kwato tarin makamai.
A karkashin Operation Whirl Punch, ya ce sojojin sun yi nasarar kashe ‘yan ta’adda 63, sun kuma kama mutane 291 da a ke zargi da kuma kubutar da masu garkuwa da mutane 62, tare da kwato tarin makamai da alburusai.
A yankin Kudu-maso-Kudu, Buba ya ce dakarun Operation Delta Safe, sun kara yawan danyen man da kasa ke hakowa a kullum zuwa sama da ganga miliyan daya da rabi a kowace rana a cikin watan Agusta.
Ya ce sojojin sun kama mutane 71 da ke satar danyen mai tare da kama lita 5,047,150 na danyen mai, lita 1,152,500 na nau’in man naurori, lita 320 na nau’in man manyan injuna da kuma lita 28,500 na man kananun abubuwan sufuri.
“Bugu da kari, sojojin sun kwato alburusai iri-iri 194 tare da lalata kwale-kwalen katako 125 da kuma wuraren tace haramtattun wurare 458.
“Duk da haka, sojoji suna yin kira da a kara nuna gaskiya da ba su ingantattun shawarwari na gwarin guiwa daga masu ruwa da tsaki a fannin tsaro da kuma hadin kai daga al’ummomin yankin.
“Sojoji kuma suna sa ido kan yadda ake hukunta masu laifin satar danyen mai,” in ji shi.
A yankin Kudu maso Gabas, Buba ya ce dakarun Operation UDO KA sun kai farmaki kan kungiyar ta’addanci ta IPOB/ESN tare da kashe ‘yan ta’adda 34, sun kama mutane 82 da a ke zargi da kuma kubutar da masu garkuwa da mutane 26. (NAN) ( www.nannews.ng )
OYS/SH
======
edita Sadiya Hamza