Shugaban kwamitin kiwon lafiya ya gargadi mata da suje gwajin ciwon daji

Shugaban kwamitin kiwon lafiya ya gargadi mata da suje gwajin ciwon daji

Spread the love

Shugaban kwamitin kiwon lafiya ya gargadi Mata da suje gwajin ciwon daji

Gwaji
Daga Awayi Kuje
Akwanga (Jihar Nasarawa), Satumba 19, 2024 (NAN) Mr Larry Ven-Bawa, Shugaban kwamitin majalisar dokokin jihar Nasarawa kan kiwon lafiya kuma memba da ke wakiltar yankin Akwanga North, ya gargadi mata da su cigaba da zuwa gwajin ciwon daji na mama da na ciki don sanin matsayinsu.

Ven-Bawa ya bada gardadin ranar alhamis a Akwanga, Jihar Nasarawa, yayin da ake bude yekuwar fadakarwar ta kwana hudu game da ciwon daji ga mata 2, 000 a gundumar Agyaga a karamar hukumar Akwanga.

Shugaban yace “ta hanyar gwajine za’a gano ciwon daji na mama saboda a ceci rayukan mata.’’

Yace za’ayi gwajegwajen a asibitin Kula da Lafiya ta Farko a yankin, ya kara da cewa “nayi tanadin magunguna, kayan aiki don ƙarfafawa tsakanin mutane, kuma a yau ina tallafa wa wannan aikin domin kare lafiyar mata.

“Zan cigaba da ba da fifiko ga lafiyar mutanen yankin Akwanga ta arewa da sauran al’umma.

“Mata da yawa sun mutu daga ciwon daji, saboda haka, ina bukatar mata su fito zuwa wannan gwaji saboda su tsare lafiyarsu.’’

Komishinan Lafiya ta Nasarawa, Likita Gwamna Gaza, da ya bude fara gwajegwajen, yace gwamnati zata cigaba da bada hankali wajen magance ciwon daji da wasu cuttuttaka a kasa.

Gaza, wanda Likita Yahaya Ubam, Sakataren Nasarawa State Health Insurance Agency (NASHIA) ya wakilta, ya yabawa Ven-Bawa saboda mahimmacin da ya baiwa lafiyar mata.

Shugabar kungiyar Mbegir Cancer Initiative, Elisha Mbegir, yace kungiyar a shirye take don kare lafiyar mata masu ciwon daji.

Ta kara da cewa gwajegwajen da za’a yi wa mata 2, 000 na kwana hudun aikin hadin gwiwa ne da kungiyar Mbegir.(NAN)(www.nannews.ng)
AKW/BRM
==========
Bashir Rabe Mani ne ya tace


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *