Shugaban ANDEF, Edwin Clark, ya rasu
Shugaban ANDEF, Edwin Clark, ya rasu
Clark
Daga Naomi Sharang
Abuja, Feb. 19, 2025 (NAN) Dattijon kuma shugaban kungiyar Pan Niger Delta Forum (PANDEF), Cif Edwin Clark, ya rasu.
Sanarwar rasuwar fitaccen shugaban na Ijaw ta fito ne a cikin wata sanarwa da iyalan suka fitar ranar Talata
mai dauke da sa hannun Farfesa C. Clark.
Sanarwar tace “Iyalan mamacin na fatan sanar da rasuwar Cif Edwin Clark
a ranar Litinin, 17 ga watan Fabrairu.
“Iyalin sun yaba da addu’o’in ku a wannan lokacin, kuma za su sanar da sauran bayanai daga baya.”
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa mutuwar Clark ta faru ne kwanaki kadan bayan
rasuwar wani shugaban kungiyar siyasa ta Pan-Yoruba, Afenifere.
Dattijon jihohin biyu sun yi fice wajen bayar da gudunmawar ci gaban kasa da kuma matsayarsu kan wasu batutuwan
da suka shafi kasa, kamar tsarin tarayya na gaskiya da sake fasalin kasa da dai sauransu. (NAN)(www.nannews.ng)
NNL/FEO/WAS
============
Francis Onyeukwu da ‘Wale Sadeeq ne suka gyara