Shugaba Tinubu ya raba tallafin taki da shinkafa ga marasa galihu a Gombe
Shugaba Tinubu ya raba tallafin taki da shinkafa ga marasa galihu a Gombe
Kyauta
Daga Hajara Leman
Gombe, Agusta 29, 2024 (NAN) Shugaban kasa Bola Tinubu, a ranar Laraba ya bayar da gudummawar tireloli guda biyu kowannen cike da shinkafa da taki ga marasa galihu a jihar Gombe.
Alhaji Saidu Alkali, Ministan Sufuri ne ya raba kayan a madadin Shugaba Tinubu.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN, ya ruwaito cewa motocin taki da shinkafa kowanne yana dauke da buhu 1,200.
Da yake jawabi a wajen taron, Alkali ya ce shugaban kasar ya yi hakan ne da nufin rage wahalhalun da masu karamin karfi ke fuskanta.
A cewar ministan, wannan karimcin wata shaida ce ta alherin da Tinubu ke nunawa al’ummar Gombe, da ya ke rike da zuciyarsa.
Da yake karbar kayayyakin a madadin gwamnatin jihar Gombe, wani dattijo kuma jigo a jam’iyyar All Progressives Congress (APC), a Gombe, Alhaji Abba Sadiq, ya nuna jin dadinsa ga shugaban kasa kan wannan karimcin.
Sadiq ya kara da cewa hakan zai taimaka matuka wajen bayar da gudunmawar bunkasa noma a jihar, da kuma tabbatar da samun isasshen abinci ga mutanen Gombe.
Ya kuma bai wa gwamnatin tarayya tabbacin cewa kayayyakin za su kai ga wadanda za su amfana. (NAN) (www.nannews.ng)
HUL/DOR
========
Nyisom Fiyigon Dore ta gyara