Shettima ya bayyana samuwar zuba jarin dala biliyan 4.8 a fannin kiwon lafiya
Shettima ya bayyana samuwar zuba jarin dala biliyan 4.8 a fannin kiwon lafiya
Lafiya
Daga Salisu Saniidris
Abuja, Agusta 31, 2024 (NAN)Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya bayyana cewa sauye-sauyen da gwamnatin tarayya ta yi a fannin kiwon lafiya ya janyo sama da dala biliyan 4.8 a bangaren zuba jari.
Da yake jawabi a wurin kaddamar da asibitocin Sahad da ke
Abuja ranar Asabar, Shettima ya bayyana wata dabarar da gwamnatin ta fitar kuma za ta
bi don magance kalubalen da suka dade da kuma ciyar da tsarin
kiwon lafiyar Najeriya gaba.
Ya kuma jaddada bukatar samun hadin kai a bangaren kiwon lafiya,
inda ya ce, “bangaren kiwon lafiyar mu na bukatar hada kai.
Irin wannan rana itace wadda ba za mu iya kau da kai ba don muhimmancin ta."
Shettima ya bayyana kudirin gwamnati na farfado da tsarin kiwon
lafiya, tare da yin gyare-gyare kan taswirar hanyar kiyon lafiya mai karfi
da a ka tsara don magance matsalolin da suka hana ci gaba.
Mataimakin shugaban kasar ya amince da kalubale a bangaren
kiwon lafiya, wadanda suka hada da hauhawar farashin magunguna,
daukar dogon lokacin jira na asibiti, da karancin ma’aikatan lafiya.
Ya jaddada mahimmancin shigar da kamfanoni masu zaman kansu
don inganta damar samun ingantaccen lafiya.
Shettima ya yabawa shugaban/wanda ya kafa kamfanin Sahad Group
of Companies, Alhaji Ibrahim Mijinyawa, bisa gudummawar da yake
bayarwa a fannin kiwon lafiya da kuma jajircewarsa na
taimamon rayukan al'umma ta hanyar sana’ar sa.
Karamin ministan lafiya da walwalar jama’a, Dr Tunji Alausa, ya
bayyana asibitin a matsayin wani sabon babi na kiwon lafiya a
Najeriya.
Ya kara da cewa kafa asibitin wani hangen nesa ne wanda ke
misalta abin da za a iya samu idan mutane masu kishin jama’a
suka zuba jari a lafiyar ‘yan kasarsu.
Mataimakin Shugaban Asibitin Sahad, Dokta Shamsuddeen Aliyu,
ya bayyana asibitin a matsayin wani gini na zamani wanda ke
nuna jajircewarsu na samar da ingantaccen kiwon lafiya.
A cewarsa, asibitin na nuni da hangen nesa don samun
kyakkyawar makoma inda kowa zai samu cikakkiyar kulawa.
Ya bayyana cewa Asibitin Sahad yana da gadaje 200 mai
dauke da dakunan tiyata guda bakwai, da injinan wankin koda
guda 13, da kuma rukunin ko ta kwana na ICU masu gadaje 10.(NAN)(www.nannews.ng)
SSI/AMM/HA
===========
Abiemwense Moru da Hadiza Mohammed-Aliyu ne suka gyara