Shahararren malamin addinin Musulunci, Dahiru Usman-Bauchi, ya rasu

Shahararren malamin addinin Musulunci, Dahiru Usman-Bauchi, ya rasu

Shahararren malamin addinin Musulunci, Dahiru Usman-Bauchi, ya rasu

Spread the love

Shahararren malamin addinin Musulunci, Dahiru Usman-Bauchi, ya rasu

Shahararren malamin addinin Musulunci, Dahiru Usman-Bauchi, ya rasu
          Shiekh Dahiru Usman Bauchi

Rasuwa
Daga Ahmed Kaigama
Bauchi, Nuwamba 28, 2025 (NAN) Shahararren malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman-Bauchi, ya rasu.

Dahiru Bauchi ya rasu da sanyin safiyar Alhamis a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, Bauchi.

Malam Ahmed Mohammed, wani daga cikin iyalansa ya tabbatar da rasuwar a ranar Alhamis a Bauchi, yace babban malamin yana karbar baki a daren Laraba, daga baya aka kai shi asibiti, inda ya rasu.

Mohammed ya kara da cewa za a yi sallar jana’iza a ranar Juma’a, Nuwamba 28, a Bauchi bisa ga al’adun Musulunci.

An dauki Dahiru Bauchi, wanda ya ma dauke da lambar Oder of the Federal Republic (OFR), a matsayin daya daga cikin manyan malaman Musulunci a Najeriya, ana tunawa da shi saboda iliminsa mai yawa, jagorancin ruhaniya da kuma sadaukar da kai ga
yada addinin Musulunci a tsawon rayuwarsa.

An haifi Usman-Bauchi a shekarar 1927 a Gombe, kuma ya sadaukar da rayuwarsa wajen ci gaban ilimin Musulunci, inganta
zaman lafiya da kuma haɓaka haɗin kai a ƙasar.

Shi ne kuma babban shugaban Tijjaniya a Najeriya, ƙungiyar Sufaye ta Musulunci. Koyarwarsa ta mayar da hankali kan tarbiyyar dabi’a, haƙuri da bin ƙa’idodin Musulunci, ta sa ya sami mabiya da yawa da girmamawa a ciki da wajen Najeriya.

Tsawon shekaru, Dahiru Bauchi ya taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban al’umma, jagoranci ga matasa, malamai da ƙarfafa fahimtar addini.

Ya bar ‘ya’ya 61 da jikoki da yawa. (NAN) (www.nannews.ng)
MAK/ RSA
=========
Rabiu Sani-Ali ne ya gyara


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *