Sarakuna na taka muhimmiyar rawa wajen samar

Sarakuna na taka muhimmiyar rawa wajen samar

Spread the love

Sarakunan na taka muhimmiyar rawa wajen samar da tsaro a Najeriya – Bayero

Tsaro

Daga Philip Yatai/Angela Atabo/Emmanuel Oloniruha

Abuja, Oktoba 3, 2024 (NAN) Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya ce Sarakuna sun kasance masu taka muhimmiyar rawa a Tsarin samar da tsaron Najeriya.

Bayero ya bayyana haka ne a Abuja ranar Alhamis a taron lacca na kasa da kasa karo na daya na Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN).

Laccar tana da taken, “Rashin tsaro a Sahel, 2008 zuwa 2024: Rarraba kalubalen Najeriya – Farawa, Tasiri da Zabuka.”

Ya shaida wa NAN a gefen taron cewa shugabannin gargajiya na kare rayuka da dukiyoyin al’umma a yankunansu.

“Hakan ya canza tsawon shekaru saboda tsoma bakin siyasa, amma har yanzu shugabannin gargajiya na da rawar da za su taka wajen kare al’ummarsu da kuma kasa,” in ji shi.

Ya bayyana cewa tsarin masarautu tun kafin lokacin mulkin mallaka, tun daga Hakimin Unguwa, Hakimin kauye, Hakimin gundumar da masarautu a sama, ya samar da wani tsari na musamman na magance matsalar rashin tsaro a matakin al’umma.

“Tsarin da aka yi shi tun kafin mulkin mallaka, don haka muna ganin idan muka koma kan haka, shugabannin gargajiya za su taka rawa wajen kare al’ummarmu.

“Ina son ‘yan Najeriya su sani cewa kowa na da rawar da zai taka wajen tabbatar tsaro a kasar nan, don haka kowa ya taka nasa rawar.

“A lokacin da kowane mutum ya taka rawar gani, na tabbata abubuwa za su yi kyau sannu a hankali,” in ji Sarkin.

Ya yabawa mahukuntan NAN kan shirya laccar wadda ya bayyana ta dace, duba da yadda rikicin yankin Sahel ya dade. (NAN) (www.nannews.ng)

FDY/ATAB/OBE/ETS

==============


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *