Sanadiyar hatsarin mota anyi asarar kankanar Naira miliyan goma a Jigawa

Sanadiyar hatsarin mota anyi asarar kankanar Naira miliyan goma a Jigawa

Spread the love

Sanadiyar hatsarin mota anyi asarar kankanar Naira miliyan goma a Jigawa

Kankana

Daga Muhammad Nasir Bashir

Dutse, Feb. 27, 2025 (NAN) Kimanin kankana Naira miliyan goma suka yi batan dabo yayin da wata babbar mota ta kife a kan titin Malamadori dake kan titin Nguru – Hadejia a jihar Jigawa.

Ana kai ‘ya’yan itatuwan da aka kiyasta kudinsu ya kai Naira miliyan daga Nguru a Yobe zuwa yankin kudancin Najeriya. 

Musa Muhammad jami’in yada labarai na karamar hukumar Malammadori ta jihar Jigawa ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Dutse.

Ya ce hadarin ya hada da wata babbar mota mai lamba FGE 592 XB.

“Wata tirela dauke da kankana ta kife a hanyar Hadejia zuwa Nguru a ranar Laraba. Motar ta fito ne daga Yobe ta nufi kudancin kasar.

“Lamarin ya faru ne da misalin karfe 9:00 na safe a tsakanin kauyukan Kachakama da Jibori,” in ji shi, inda ya kara da cewa wani rahoton farko da aka fitar ya alakanta hadarin da gudun wuce kima.

Ya ce direban motar Ahmed Ibrahim da mataimakinsa sun samu raunuka daban-daban, inda a ka garzaya da babban asibitin Hadejia domin yi musu magani.

Musa ya ce jami’an hukumar kiyaye haddura (FRSC), sun gudanar da aikin ceto tare da share hanyar domin saukaka zirga-zirgar ababen hawa.

Da aka tuntubi kakakin hukumar FRSC a jihar, Yahaya Ibrahim, ya tabbatar da faruwar lamarin. (NAN) (www.nannews.ng)

MNB/RSA

=======

Rabiu Sani-Ali ya gyara 


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *