Ramadan: Kungiya ta yaba da tallafin da Ministan tsaro ke bayarwa a Sokoto, Kebbi, Zamfara
Ramadan: Kungiya ta yaba da tallafin da Ministan tsaro ke bayarwa a Sokoto, Kebbi, Zamfara
Taimako
Daga Habibu Harisu
Sokoto, Maris 17, 2025 (NAN) Wata Kungiyar kwararrun musulmi ta yaba da goyon bayan da karamin ministan tsaro, Bello Matawalle yake ba wa masu karamin karfi a jihohin Sokoto, Kebbi da Zamfara.
Shugaban kungiyar, Farfesa Mika’il Jibrin, ya yi wannan yabon ne a wata hira da manema labarai a ranar Litinin a Sokoto.
Jibrin ya ce Naira miliyan 500 tare da kayan abinci da Matawalle ke rabawa a matsayin tallafin watan Ramadan ya zama tushen taimakon ‘yan kasa don haka ya bukaci masu hannu da shuni da su yi koyi da hakan.
A cewarsa, ko shakka babu wannan matakin zai rage wahalhalun da akasarin al’ummar Zamfara ke fuskanta da sauran jihohin Arewa maso Yamma.
Ya ce matakin na ministan ya kai ga jama’a a fadin kananan hukumomin jihar 14, inda hakan ya kawo karshen matsalolin tattalin arziki a lokacin azumin watan Ramadan.
Jibrin ya ce ‘ya’yan kungiyar sun fara ziyarar duba rabon kayan abinci da kudaden sun isa cibiyoyin da aka yi niyya ga marasa galihu a karkashin ‘Ramadan Free Meals Initiative’ a jihohin Zamfara da Sokoto.
Yayin da ya ke bayyana wannan al’amari a matsayin gagarumin aikin agajin, Jibrin ya ce ta amfana matuka ga iyalai masu karamin karfi, marayu, ‘yan gudun hijira da gidajen marayu a wurare da dama a fadin jihar Zamfara da sauran jihohi.
Kungiyar ta bukaci wadanda suka ci gajiyar shirin da su yaba da wannan karimcin ta hanyar yin addu’o’in samun hadin kan al’umma, zaman lafiya da samun nasara wajen yaki da kalubalen tsaro da ke addabar kasar. (NAN) (www.nannews.ng)
HMH/KLM
========
Muhammad Lawal ne ya gyara