PCN ta rufe shagunan sayar da magunguna 581 a Adamawa

PCN ta rufe shagunan sayar da magunguna 581 a Adamawa

Spread the love

PCN ta rufe shagunan sayar da magunguna 581 a Adamawa

Magani

Daga Ibrahim Kado

Yola, Satumba 20, 2024 (NAN) Majalisar harhada magunguna ta Najeriya (PCN) ta rufe shagunan sayar da magunguna 581 a jihar Adamawa saboda sabawa dokokin aiki.

Mista Stephen Esumobi, Darakta mai tabbatar da doka na majalisar ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Yola ranar Juma’a.

Ya ce an rufe wuraren ne a lokacin da jami’an tsaro da maikatan majalisar suka ziyarci shagunan magunguna da su ka kai 816 a fadin jihar.

Ya lissafo kananan hukumomin da suka ziyarta da suka hada da Yola ta Arewa da Yola ta Kudu da Mubi ta Arewa da Mubi ta Kudu da Girei da Numan da Michika da kuma Demsa.

“Gidajen da aka rufe sun hada da kantin magani 35, shagunan sayar da magunguna 325 da shagunan sayar da magunguna ba bisa ka’ida ba 221,” in ji Esumobi.

Daraktan ya bayyana cewa yanayin da ake ajiye magungunan da yawa daga cikin wuraren bai wadatar ba, wanda hakan ke sanya magunguna cikin tsananin zafi. 

A cewarsa, irin wadannan magunguna za su lalace kuma su zama marasa dacewa da amfani ga dan Adam.

“Hakazalika, da yawa daga cikin kantin magani ba su da ƙwararrun likitocin da za su kula da rarraba magungunan da sauran samfuran abubua tare da ƙarancin tsari, yayin da masu siyar da kayayyaki ke yin kasuwancin da ya sabawa doka.

“Bugu da ƙari, wurare da yawa suna aiki a wuraren da ba su dace da kasuwancin magunguna ba kuma an nemi su canza wuraren, ” in ji shi.

Esumobi ya nuna damuwarsa kan yadda aka hukunta da yawa daga cikin wadanda suka gaza yin aikin a shekarar 2022, amma sun ki gyara matsalar.

Ya umurci jami’in PCN na jihar da ya ci gaba da sa ido sosai a kan cibiyoyin harhada magunguna don tabbatar da bin ka’idojin aiki, da kuma masu aikata laifuffuka.(www.nannews.ng)(NAN) IMK/NB/SOA

Nabilu Balarabe/Oluwole Sogunle ne ya gyara shi

 


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *