Nnamdi Kanu ya kori kungiyar lauyoyi masu kare shi, ya kalubalanci hurumin kotu
By Taiye Agbaje
Abuja, Oktoba 23, 2025 (NAN) Nnamdi Kanu, shugaban masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB), a ranar Alhamis, ya bayyana korar tawagar lauyoyinsa, karkashin jagorancin Cif Kanu Again, SAN, a babbar kotun tarayya dake Abuja.
Kanu, ya shaida wa mai shari’a James Omotosho, a zaman da aka ci gaba da zaman, cewa a shirye yake ya kare kansa.
Biyo bayan matakin da shugaban kungiyar ta IPOB ya dauka, dukkan manyan masu fafutuka a cikin kungiyar da suka hada da Cif Agabi, tsohon babban lauyan gwamnatin tarayya (AGF), sun janye daga ci gaba da fitowarsu a shari’ar.
Dangane da wannan al’amari, Kanu, wanda a yake gabatar da jawabi a gaban kotun, ya kalubalanci hurumin kotun da ta gurfanar da shi.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN), ya ruwaito cewa Kanu ya sanya hannu a kan korafinsa kuma ya shigar da shi a ranar 21 ga watan Oktoba.
Ya kuma sanya tsohon babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami da sauran su, a matsayin shaidu a ci gaba da shari’ar da ake yi na zargin ta’addanci, kuma ya jera manyan mutane da dama a matsayin shaidu.
Daga cikin wadanda Kanu ya lissafa a matsayin “shaidu masu karfi” akwai Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike; tsohon ministan tsaro, Janar Theophilus Danjuma mai ritaya da kuma tsohon babban hafsan sojin kasa, Janar Tukur Buratai mai ritaya.
Sauran sun hada da, Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas, Gwamna Hope Uzodinma na Imo, ministan ayyuka, Dave Umahi, tsohon Gwamnan Abia, Okezie Ikpeazu, da tsohon Darakta-Janar, Hukumar Leken Asiri ta (NIA), Ahmed Abubakar.
Sauran sun hada da tsohon shugaban hukumar tsaro ta farin kaya, Yusuf Bichi, da kuma shaidu da dama da bai bayyana sunayensu ba.
Kanu, a cikin karar, ya yi alkawarin gabatar da bayanan rantsuwar dukkan shaidun, na son rai ga wannan kotu mai girma, kuma za su sanar da masu gabatar da kara a lokacin da ya dace.
Hakazalika, NAN ta ruwaito cewa shugaban na IPOB ya yi ganawar sirri da tawagar lauyoyin sa a babbar kotun kasa a Abuja ranar Laraba.
Kanu wanda jami’an hukumar tsaro na farin kaya (DSS) suka gabatar da shi a kotu, ya gana da ‘yan kungiyar llauyoyin nasa a kotun mai shari’a James Omotosho, kamar yadda aka umarta a baya.(NAN)(www.nannews.ng)
TOA/SH
Fassarar Aisha Ahmed
=====

