NHIA da Kamfanin Magunguna na Roche sun tallafa wa masu ciwon daji a Bauchi
NHIA da Kamfanin Magunguna na Roche sun tallafa wa masu ciwon daji a Bauchi
Ciwon Daji
Daga Amina Ahmed
Bauchi, Yuli 30, 2025 (NAN) Hukumar Kula da Inshorar Lafiya ta Kasa (NHIA) ta kaddamar da hadin gwiwa tsakanin
ta da Kamfanin Magunguna na Roche da Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH) ta Bauchi,
domin tallafawa masu fama da ciwon daji ta hanyar tsarin rabon kudin magani.

Shugaban NHIA a jihar Bauchi, Malam Mustapha Mohammed, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ranar Laraba a Bauchi cewa an tattauna hanyoyin aiwatar da shirin a wani taron hadin gwiwa da aka gudanar.
A cewarsa, karkashin tsarin rabon kudin maganin, NHIA za ta dauki nauyin kaso 30 na kudin magani, kamfanin Roche zata biya kaso 50, yayin da majinyata za su dauki nauyin kaso 20.
Ya ce “ga wadanda ba su yi rajista a karkashin NHIA ba, za a raba kudin magani tsakanin su da Roche; Roche za ta dauki kaso 50, su kuma su dauki sauran kaso 50.
“Wadanda suka yi rajista da NHIA za su fara samun kulawa bayan wata biyu.”
Dr Haruna Usman, Shugaban Kwamitin Ba da Shawara na Likitoci a ATBUTH, ya bayyana wannan hadin gwiwa a matsayin babbar nasara wajen dakile yawaitar cutar daji a yankin.
Ya ce asibitin ta inganta tsarin tattara bayanai ta hanyar sabbin fasahohin e-health.
Ya kara da cewa “zaben ATBUTH a wannan shiri ya dace kwarai, domin asibitin ta samu sauye-sauye masu ma’ana a bangaren bincike, ayyukan jinya, da horar da ma’aikata.”
Usman ya nuna godiya ga Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya, NHIA, da Kamfanin Roche bisa hadin gwiwar su wajen yaki da cutar daji a Najeriya.(NAN)(www.nannews.ng)
AE/HA
=======
Hadiza Mohammed-Aliyu ce ta gyara
AE/HA
=======
Hadiza Mohammed-Aliyu ce ta gyara