Najeriya ta yi rashin dan kishin kasa Audu Ogbeh – Tinubu

Najeriya ta yi rashin dan kishin kasa Audu Ogbeh – Tinubu

Spread the love

Najeriya ta yi rashin dan kishin kasa Audu Ogbeh – Tinubu

Ogbeh
Daga Muhyideen Jimoh
Abuja, 9 ga Afrilu, 2025 (NAN) Shugaban kasa Bola Tinubu ya jajanta rasuwar Cif Audu Ogbeh, tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, yana mai bayyana shi a matsayin babban dan kishin kasa.

Ogbeh, mai shekaru 78, ya rasu ne cikin kwanciyar hankali a ranar Asabar, kamar yadda wata sanarwa daga iyalansa ta bayyana.

A cikin sakon ta’aziyyar da mai magana da yawunsa Mista Bayo Onanuga ya aike, Tinubu ya jajanta wa gwamnati da al’ummar jihar Binuwai.

Shugaban ya kuma mika ta’aziyyarsa ga iyalai da abokan arziki da kuma abokan siyasa Ogbeh.

Ogbeh, ya yi wa Najeriya hidima a gwamnatoci da dama, ciki har da ministan sadarwa a jamhuriya ta biyu, sannan kuma ya zama ministan noma a karkashin shugaba Muhammadu Buhari.

Tinubu ya yaba wa zurfin basirar Ogbeh da kuma yadda yake tsara hanyoyin magance matsalolin kasa.

Ya lura cewa Ogbeh ya fara siyasa a shekarun 1970 a matsayin dan majalisa kuma ya kasance dan jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

“Cif Audu Ogbeh mutum ne mai kishin kasa wanda hikimarsa, kwazo da neman ci gaba ya bar tabarbarewar siyasa a Najeriya.”

“Ya kasance a shirye koyaushe da gaskiya da alkaluma don tallafawa  shawarwarinsa. Al’ummar kasar za su yi matukar kewar hangen nesansa da kuma kwarewarsa,” in ji Tinubu.

Shugaban ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu, ya kuma baiwa iyalansa lafiya. (NAN)(www.nannews.ng)
MUYI/SH

=======
Sadiya Hamza ta gyara


Spread the love

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *