Na gina gida, ina samun N150,000 duk wata daga sana’ar ban dakin jama’a, inji wani mutumin Gombe
Na gina gida, ina samun N150,000 duk wata daga sana’ar ban dakin jama’a, inji wani mutumin Gombe
Ban Daki
Daga Peter Uwumarogie
Gombe, 22, ga Yuli, 2025 (NAN) Malam Khalid Umar, mai sana’ar ban dakin jama’a a Jihar Gombe, ya ce ya yi nasarar gina gida kuma yanzu haka yana samun
fiye da N150,000 a duk wata daga gudanar da gidajen ban dakin jama’ar sa a cikin birnin Gombe.
Umar, wanda ya bayyana hakan a cikin wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Gombe ranar Litinin, ya ce kasuwancin
ya taimaka masa wajen cika bukatun iyalinsa.
Ya ce ya dade yana gudanar da kasuwancin gidan ban daki shekaru 35 da suka gabata, kuma a cikin wannan lokacin, ya samu nasarori da yawa kuma
ya saka kudaden da ya samu cikin wasu sana’o’i don samun karin kudaden shiga.
A cewarsa, yana da dakin ban daki guda takwas da dakin wanka guda tara a babban kasuwar Gombe.
Ya kara da cewa wannan kasuwancin shine tushen kudaden shiga na sa inda yake samun kudi don kula da matarsa da ‘ya’ya takwas da dukkansu ke zuwa
makaranta.
Ya ce “ wannan kasuwancin yana da kyau kuma shine babban tushen kudina na tsawon shekaru, saboda na gina gidana na kaina kuma ina kula da bukatun iyalina.
“Ina samun fiye da N150,000 a kowane wata kuma a kowace rana ina samun tsakanin N4,000 da N8,000 bisa ga yadda kasuwancin ta kasance a ranar.
“Ina godiya wa Allah cewa mutane suna amfani da bandakina duk lokacin da bukatarsu ta taso.”
Umar, ya ce shima ya samu damar ci gaba da karatunsa bayan makarantar sakandare wajen samun diploma a Harkokin Musulunci.
Ya ce ba shi da nadama wajen shiga wannan kasuwancin, duk da bambancin da ya fuskanta tsawon shekaru, inda mutane ke yawan zargin shi da yin aikin
da suka dauka a matsayin gurbatacce.
Ya yi kira ga gwamnatin jihar Gombe da sauran masu ruwa da tsaki su zuba jari a gudanar da tsaftace gari don inganta lafiyar jama’a, kirkiro ayyuka da
arziki ga matasa.
Ya bukaci gwamnatin jihar da ta kafa wani tsarin Sarrafa Shara a fadin jihar.
“Idan an tsabtace zubar da as shara yadda ya kamata, matakin zai iya taimakawa wajen inganta lafiyar ƙasa da ƙara habaka aikin gona ba
tare da haifar da barazanar lafiya ba,” in ji shi.(NAN)(www.nannews.ng)
UP/HA
=======
Hadiza Mohammed-Aliyu ce ta gyara